Connect with us

Politics

Atiku Da Obi Sun Caccaki Shugaba Tinubu Kan Kalamansa Na “Ba Talakawan Nijeriya Kaɗai Ke Talauci Ba”

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, Atiku Abubakar, da jam’iyyar Labour sun caccaki shugaba Bola Ahmed Tinubu da cewa ba Nijeriya ce kaɗai ke fuskantar irin wannan matsanancin yanayi da ake ciki ba.

Idan za a iya tunawa, Tinubu a lokacin da yake karɓar tawagar ‘yan majalisar dokokin ƙasar da suka zo taya shi murnan bikin Babbar Sallah, a daren ranar Litinin, ya ce, duk da cewa akwai talauci da wahalhalu a ƙasar, ba Nijeriya ce kaɗai ke fuskantar irin wannan matsalar ba, inda ya gargaɗi masu laifi kan lalata hanyoyin jirgin ƙasa, da satar igiyoyin lantarki, satar ɗanyen fetur, yana mai bayyana irin waɗannan ayyuka a matsayin zagon ƙasa ga Nijeriya.

Advertisement

Abinda Atiku Abubakar Da Kuma Muhammadu Buhari Suka Tattauna Yayin Ganawarsu A Daura

Ya kuma ce, mawuyacin hali na tattalin arziki shi ne ƙalubalen da gwamnatinsa ke fuskanta, inda ya ce duk wahala da ƙalubale ba zai juya wa Nijeriya baya ba.

“Eh, akwai talauci; akwai wahala a cikin ƙasa. Ba mu ne kawai mutanen da ke fuskantar irin wannan ba amma dole ne mu fuskanci ƙalubalenmu. Dole ne mu nemo hanyar kawar da ‘yan bindiga da ta’addanci ta yadda manoma za su iya fitar da abinci daga filayen noma.

“Akwai buƙatar dakatar da fasa kwauri da duk wani zagon ƙasa na tattalin arziki. Me ke sa mutane su cire hanyoyin jirgin ƙasa, satar igiyoyin lantarki da zagon ƙasa ga tattalin arziki? Dole ne mu rungumi gaskiya don canja tsarin mu.

Advertisement

“Idan har muna so mu ji daɗi, dole ne mu canja tunaninmu game da ƙasarmu,” inji Shugaba Tinubu.

Ya yaba wa shugabannin majalisar dokokin ƙasar bisa goyon bayan da suke baiwa gwamnatinsa, wanda ya haifar da wasu muhimman cigaban da ta samu.

“Abin alfahari ne a gare ni in sami mafi kyawun abokan tarayya a Majalisar Dokoki ta ƙasa. Dole ne mu kasance masu haɗa kai a yunƙurinmu na gamsar da jama’armu. Abu ne mai ban tsoro, amma ba za mu iya guje wa gaskiyar cewa dole ne asar nan ta tsira daga wahalhalu ba,” inji Shugaban.

Advertisement

Da ta ke mayar da martani, jami’iyyar LP ta bayyana rashin jin daɗinta da kalaman shugaba Tinubu, wanda ta bayyana a matsayin ‘izgili’ ga talakawan Nijeriya.

Sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na ƙasa, Obiora Ifoh, a wata zantawa da ya yi da jaridar Ɓanguard, ya ce akwai buƙatar a tuna wa shugaban asa cewa an zaɓe shi ne domin ya ragewa, idan ma bai iya kawar da talauci baki ɗaya ba, ba ƙara ta’azzara shi ba.

Ifoh ya ce: “Mun ji takaici amma ba mu yi mamakin kalaman da Shugaba Bola Tinubu ya yi ba game da tsananin talauci da manufofin gwamnatinsa suka jefa ‘yan Nijeriya tun bayan hawansa mulki sama da shekara guda da ta wuce.

Advertisement

“Abin takaici ne idan aka ji shugaban aasa yana izgili ga ‘yan ƙaarsa da cewa ba ‘yan Nijeriya ne kaɗai ke fuskantar talauci ba.

“Shugaban ƙasa, muna roƙonka da ka kiyaye kundin tsarin mulkin da ka rantse da shi. Kundin tsarin mulkin ƙasar ya ce tsaro da jin daɗin jama’a shi ne babban dalilin wanzuwar gwamnatin ka. Wannan izgili ya isa haka.”

Da ya ke jawabi a makamancin haka, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, ta bakin mai ba shi shawara na musamman, Paul Ibe, ya ce: “bai dace Tinubu ya yi irin wannan furuci ba”.

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *