Connect with us

News

Gwamna Caleb Mutfwang Ya Haramtawa Masallatai da Coci-coci Toshe Hanyoyi

Published

on

Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato ya haramtawa duk wasu cibiyoyin addini da ke Jihar rufe tituna a lokacin ibada.

Gwamnan ya kuma buƙaci daukacin Shugabannin cibiyoyin addinan da su nuna shaidar amincewar ginin Masallatai da Coci-coci ga hukumar ci gaban birnin Jos (JMDB) kuma su fuskanci hukunci.

Advertisement

Hanyoyin  Kare Kai Daga Kamuwa Da Cutar Kwalara

A wata wasika mai kwanan wata 13 ga watan Yunin 2024, kuma babban Manajan hukumar Hart Bankat ya sanya wa hannu, Gwamnatin ta ce matakin na daga cikin aiwatar da umarnin zartarwa na 003 wanda Gwamna Mutfwang ya sanya wa hannu.

Rahotanni na nuni da cewa Takardar da aka fitar a ranar Asabar an aikata zuwa ga Shugabannin kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen Jos, da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) na Jihar.

Sakataren Jama’atu Nasrul-islam na Jihar Dr Salim Musa Umar ya karɓi Takardar.

Advertisement

Wani ɓangare na wasikar ya ce “Bisa umarnin zartarwa mai lamba 003 na Gwamnan Jihar Filato, Barista Caleb Mutfwang ya sanyawa hannu a ranar 1 ga watan Maris 2024 don kula da zirga-zirgar ababen hawa da Gine-gine, Ina Umartar daina toshe hanyoyin zirga-zirga a duk wuraren ibada. Yakamata a samar da wuraren ajiye motoci wadatacce nesa da manyan tituna yayin ibada.

Ya kamata dukkan cibiyoyin Ibada su samar da shaidar amincewar gininsu ga hukumar raya Birnin Jos don gujewa hukunci daga Gwamnati.

Don haka shugabannin su taimaka wajen ba mambobinsu shawara su zama masu bin doka da oda don karfafa musu gwiwa su bi dokokin da aka gindaya.”

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *