Connect with us

News

Hanyoyin  Kare Kai Daga Kamuwa Da Cutar Kwalara

Published

on

Spread the love

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Kamar yadda aka sani damina ta Kunno Kai wanda shine lokacin da cutuka irin su Kwalara suka fi yaɗuwa a cikin al’umma,Hakan ne ya sa Gwamnatin tarayya ta shawarci ƴan Najeriya da su yi ƙoƙarin tsaftace kansu da kuma muhallin su domin dakile yaɗuwar cutar a faɗin ƙasar.

Babban Sakatare a Ma’aikatar Muhalli, Mahmud Kambari, shi ne ya yi jawabin a ranar Asabar a wajen wani taron tunawa da ranar tsaftar muhalli ta kasa na shekarar 2024 da aka yi a garin Piwoyi da ke Abuja

Advertisement

Barayi Sun Balle Tagar Wani Masallaci Sun Sace Batur A Kano 

Kamar yadda aka saba Ana gudanar da ranar tsaftar muhalli ta ƙasa a ranar 28 ga watan Yunin kowace shekara domin ganin an wayar da kan ƴak Najeriya game da mahimmancin tsaftar jiki da na muhalli.

Wikki Times ta ruwaito cewa Jawabi ya cigaba da cewa manufar shirin shi ne wayar da kan al’ummar Najeriya kan mahimmancin tsaftar muhalli a matsayin sahihiyar hanyar shawo kan cututtuka masu yaduwa.domin kare yaɗuwar wannan cuta Akwai hanyoyi daban daban kamar haka:

Manyan hanyoyin kare kai daga yaɗuwa da cutar ta kwalara shine shawo kan amfani da gurɓataccen ruwa ko abinci .

Advertisement

Tsaftace muhalli musamman wajen cin da kuma dafa abinci , Bayangida,da sauran wurare na aiki a cikin gida

Wanke hannaye kafin cin abinci yana taimakawa sosai wajen daƙile cutar kwalara a cikin jikin ɗan Adam.

Haka kuma kafin a ci abinci yana da kyau a sake farashi sosai kafin a ci. Ingantacciyyar tsafta na taimakawa wajen daƙile Kwalara

Advertisement

Wanke ƴaƴan itatuwa kafin a kai baki yana da matukar tasiri wajen taimakawa a yaƙi cutar Kwalara.

Sai dai Hukumar dake dakile yaduwar cuttukka ta Nijeriya NCDC tace bata da wadatacciyar Allurar ragakafin cutar kwalara.

Daraktan hukumar Dr. Jide Idris ne ya bayyana hakan, inda yace kasar ta bayar da sallahun allurar ga hukumomin dake da alhakin sayar da ita a duniya da masu bayar da tallafinta, duk da cewa bai bayyana ranar da allurar zata iso ba.

Advertisement

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rahotannin ke bayyana yadda mutane 40 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar ta kwalara a kasar nan kamar yanda Jaridar PR NIGERIA ta ruwaito

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *