Connect with us

News

Kungiyar tsofaffin dalibai ku rinka tallafawa junan ku – KABIR BASIRU FULATAN 

Published

on

Tsofaffin dalibai ta Mass Communication Students Association (MACOSA) Class 2020 Kano State Polytechnic sun gudanar da taronsu na shekara domin sada zumunci a tsakaninsu.
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kungiyar tsofaffin dalibai ta Mass Communication Students Association (MACOSA) Class 2020 Kano State Polytechnic sun gudanar da taronsu na shekara domin sada zumunci a tsakaninsu.

Shugaban Jaridar INDA RANKA KABIRU BASIRU FULATAN ya bayyana Sada zumunta a tsakanin Mutane Abu ne da yake kara tsawon Rayuwa a duniya musamman ayi shi saboda Allah

Advertisement

Tsofaffin Dalibai Suna Da Rawar Da Zasu Taka Wajen Gyaran Makaranta —Malam Alhassan 

.
Fulatan ya bayyana hakan a yayin Taron kungiyar tsofaffin daliban koyon aikin jarida na Makarantar Kano State Polytechnic aji na 2020.

Ya bayyana muhimmancin zumunci musamman sada zumunta a tsakanin dalibai.da kusan shine a yanzu kusan hanyar sada zumunci Mai sauki da Kuma Tarin lada da Kuma tasiri

Haka zalika ya yabawa wa kungiyar aji na 2020 a matsayin zakaran gwajin dafi wajen sada zumunta musamman yadda suka kula da junan su

Advertisement

Shima a nasa jawabin Shugaban kungiyar tsofffin daliban aji na 2020 Sulaiman Yakubu Zakirai ya bayyana makasudin shirya Taron inda yace dama duk shekara suna gudanar da taran tsaffin dalibai domin a tattauna mahimmancin batutuwan da suka shafi daliba

Ya Kara da cewa a wannan lokacin akwai rawar da tsofaffin dalibai zasu taka wajen ganin rayuwar dalibai ta inganta musamman ma a gyaran Makarantar don inganta harkokin ilimi.

Shima a nasa jawabin daya daga cikin ya manyan dalibai komarade Misbahu Yakubu ya bayyana cewa taron na yan aji na 2020 dama su kanyi don sada zumunci da taimakon juna duk shekara.

Advertisement

Ya ce yanzu haka a yan ajin nasu akwai Yan Jaridu da dama, Haka zalika ya kamata a bada hadin Kai da yin iya kokari duk lokacin da aka nemi za’ayi wani abu ko taro Ko rashin lafiya ta kama wani ko rasuwa kowa na iya kokarinsa Dan taimakawa.

Misbahu yakubu ya yi kira ga mambobinsu akan su kara zage damtse akan irin taimakon,da suke na cigaban ilimi, domin a halinda ake ciki Gwamnati ba za ta iya ita kadai ba, sai masu ruwa da tsaki sun shigo ciki. Al,umma

Advertisement
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *