Politics
Jam’iyyar NNPP Ta Sanar Da Ranar Ƙarshe Ga Duk Wanda Yake Da Ra’ayin Tsayawa Takara A Zaɓen Ƙananan Hukumomi
Jam’iyyar NNPP a nan Kano ta sanya 31 ga watan Agusta a matsayin wa’adin ƙarshe ga duk wanda yake da ra’ayin tsayawa takara a zaɓen ƙananun hukumomin kuma yake riƙe da wani muƙami na Gwamnati da ya ajje aiki kafin cikar wa’adin.
Shugaban jam’iyyar ta NNPP a Kano Sulaiman Hashim Dungurawa shi ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema Labarai da ya gabatar yau a ofishin jam’iyyar dake titin Lugard.
Yace duk wanda ke da ra’ayin tsayawa takara ya zama wajibi ya ajiye duk wani aiki ko muƙamin gwamnati da yake da shi, kamar yadda dokar hukumar zabe ta tanada.
Haka zalika kuɗin takara da Hukumar zabe ta sanya, shugaban jam’iyyar yace sun karɓa hannu Biyu, kuma suma a matakin jam’iyya tuni suka sanya nasu kuɗin na fom ga duk wanda yake da ra’ayin tsayawa takara.
Hashim Dungurawa ya ce zasu gabatar da zaben cikin gida domin fitar da Ƴan takara, su kuma mikawa Hukumar Zaɓe sunayen yan takarar duk a cikin watan Satumba maizuwa.