Business
Yadda CBN Ya Ƙaƙaba Wa Masu POS Ƙa’idoji Da Dabaibayin Yin Hada-hadar Kuɗaɗe
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fitar da sanarwa mai ɗauke da ƙa’idoji, sharuɗɗa da dokin umartar masu kamfanonin hada-hadar kuɗaɗe na zamani (PSPs) cewa su gaggauta ɗora manhajar POS cikin sanhon tattara bayanan hada-hadar kuɗaɗe na PTSA, domin a riƙa sa-ido da bibiyar dukkan hanyoyin da ake aikawa ko karɓar kuɗi ta hanyar yanar gizo a Najeriya.
Wannan umarni ya biyo bayan bada lasisi na Tsarin Taskace Hada-hadar Kuɗaɗe na Bai-ɗaya (UPLS) a watan Afrilu, wanda aka fito da shi domin magance damuwar da ake yi dangane da yadda za a taskace biyan kuɗaɗe a POS cikin manhajar sanhon killace bayanai ɗaya tilo.
Akwai Yiwuwar Barkewar Annobar Cutar Farankama A Najeriya – Hukumomin Lafiya
Sanarwar wadda CBN ya fitar a ranar 11 ga Satumba, mai ɗauke da sa hannun Daraktan Kula da Tsare-tsaren Biyan Kuɗaɗe na Bankin, Oladimeji Taiwo, ta bayyana cewa CBN ya umarci cewa daga yanzu duk wasu kuɗaɗen da za a tura ta hanyar POS tilas sai a ƙarƙashin kamfanin PTSA mai rajista da kuma lasisi daga CBN ɗin.
PREMIUM TIMES ta ruwaito cewa akwai kamfanonin hada-hadar kuɗaɗen da ba su da rajista da CBN, kuma su na tasarifin kuɗaɗe ta hanyar POS.
Mohammed Muhammad ya je zai buɗe sabon asusun banki cikin watan Yuni, sai mai POS ya ce masa, “kamata ya yi ka buɗe Opay ko Money Point, domin a gaskiya Palmpay da ka ke son ɓugewa, ba shi da rajista da CBN.”
Sai dai kuma ba a sani ba ko Palmpay ɗin ya yi rajista da CBN bayan wancan lokacin