News
Kasurgumin Ɗan Bindiga, Bello Turji Ya Gindaya Sharuɗdan Kawo Karshen Harare Da Yake Jagoranta
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Shahararren ɗan bindigar nan da ya yi ƙaurin suna wajen satar mutane da karɓar kuɗin fansa, Bello Turji, ya zargi gwamnan Zamfara Dauda Lawal da tsohon gwamnan jihar kuma ƙaramin ministan tsaron Najeriya, Bello Matwalle da siyasantar da batun tsaro a jihar.
Bello Turji wanda ake zargin ya yi ƙaura daga jihar Zamfara tun bayan tsananta hare-hare da rundunar sojin Najeriya ke yi, ya gindaya sharuɗa da za a bi wajen samar da zaman lafiya a jihar.
Bello Turji ya ce za a samu zaman lafiya a jihar ne idan jami’an tsaro da ‘yan bijilanti suka daina kashe Fulani a jihar da ma sauran johohi.
Ya bayyana hakan ne cikin wani faifan bidiyo da ya saki a ranar Litinin, inda aka nuna shi zaune a kan sabon babur riƙe da bindiga da kuma wata bindigar da ke jingine a kusa da shi.
Wasan yaran da gwamnan Zamfara na yanzu da magabacinsa ke yi ba komai ba ne face siyasa domin dukkansu ba sa kishin mutanen jihar.
“Ina son mutanen Zamfara su fahimci cewa, sun (gwamna Dauda da Matawalle) ‘yan siyasa ne da ba sa kishin al’ummarsu,” a cewar Bello Turji.
“a lokacin da Matwalle ke gwamna, waye yake ɗaukar nauyinmu? Haka kuma a lokacin da Abdulaziz Yari ke gwamna, wa yake ɗaukar nauyinmu? Ba wanda ke ɗaukar nauyinmu ban da Allah,” Bello Turji, ya faɗa a yayin da yake mayar da martani.
Ya ce batun ‘yan bindiga ya samo asali tun kafin zuwan Dauda Lawan Dare da kuma Matawalle domin ya samo asali ne a lokacin gwamna Ahmed Yerima.
“A lokacin gwamna Yerima, ya sayar da filayen da bisa doka na Fulani ne da suke noman dabbobinsu. A lokacin da Muhmud Shinkafi ya zo, ya yi ƙoƙarin warware matsalar, amma bai yi nasara ba. Haka Abdulaziz Yari wanda ya tallafawa ‘yan bijilanti, amma har zuwa yanzu ga shi muna ta gwagwarmaya,” Turji ya faɗa.
“Shi ya sa muke kiran dukkaninku da ku zo mu haɗa kai domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa da dakatar da zubar da jini. Harbi da ruwan bamabamai ba zai dakatar da mu ba domin ba ma tsoron mutuwa.
Sai dai ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara ba, Muhammad Lawal, da kuma takwaransa na ƙaramin ministan tsaro ba, Ahmad Dan-Wudil ba ta waya domin bayyana ra’ayinsu kan wannan kalamai na Turji.
GAME DA MUTUWAR SUBUBU:
Bello Turji ya tabbatar da kashe Halilu Sububu wanda ya bayyana da mai gidansa da cewa ba hakan ba zai sagar wa a ‘yan bayansa guiwa ba, za su cigaba kai munanan hare-hare a kan mutane a jihohin Zamfara da Sokoto da Katsina da Neja ba.