Business
Matatar Dangote Ta Nemi Kotu Ta Soke Lasisin Shigo Da Mai Na NNPC, Matrix A.A. Rano, Da Wasu Kamfanoni Guda Huɗu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Matatar Mai ta Dangote ta nemi Kotu ta soke lasisin shigo da Mai Na NNPC, Matrix A.A. Rano, da Wasu kamfanoni Guda huɗu
Bugu da ƙari, Matatar Dangote na neman diyya ta Naira Biliyan 100 daga NMDPRA saboda ci gaba da bayar da lasisin shigo da kayayyaki ga NNPCL da sauran kamfanoni guda hudu.
Gwamnan Katsina Ya Bayar Da Umarnin Rufe Makarantun Koyon Aikin Lafiya Masu Zaman Kansu
Matatar Dangote ta kai ƙara a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja Domin a soke lasisin shigo da kayayyaki da aka bai wa NNPC, Matrix Petroleum Services Limited, A. A. Rano, “duk da cewa Matatar Dangote tana samar da AGO da Jet-A1 fiye da bukatar yau da kullum na man fetur a Najeriya.”
A cikin shari’ar mai lamba FHC/ABJ/CS/1324/2024, Matatar Dangote tana neman diyya ta Naira biliyan 100 daga NMDPRA. Ta zargi cewa NMDPRA tana ba da lasisin shigo da kayayyaki ga NNPCL, Matrix Energy, da sauran kamfanoni ba bisa ka’ida ba, don shigo da kayayyakin fetur, ciki har da AGO da man jirgin sama zuwa Najeriya.