News
Gurfanar Da Yara Ƙanana A Gaban Kotu Abun Kunya Ne Ga Dimokradiyya Najeriya –Shehu Sani
DAFA KABIRU BASIRU FULATAN
Tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya yi Allah-wadai da matakin gurfanar da yara kanana a gaban kotu kan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Najeriya.
An gurfanar da masu zanga-zangar tsadar rayuwa da yunwa wanda yara ƙanana ne a gaban kotu ranar Juma’a.
Dokar Yancin Yara Bata Yarda A Gabatar Da Yara A Gaban Babbar Kotu — Lauya
Rahotanni na nuni da cewa biyu daga cikin yaran sun yanke jiki sun faɗi a harabar kotun.
Yan Najeriya da suka haɗa da wasu lauyoyi sun caccaki matakin tare da sukar Gwamnatin Tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Da yake mayar da martani a dandalin Sadarwa na X, Sanata Sani ya bayyana tuhumar da ake yi wa kananan yara a matsayin abin takaici kuma abun kunya ga dimokradiyyar Najeriya.
Ya kuma buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta janye tuhumar da ake yi musu kuma ta mayar da su Jihohinsu.
Tsara shigar da waɗannan yara ƙanana a zanga-zanga abin takaici ne kuma abin kunya ne ga dimokuradiyyar kasarmu.
“Ya kamata Gwamnatin ta janye tuhumar da ake musu kuma ta mayar da su jihohinsu,” in ji shi.