News
Sabon Ministan Ilimi Ya Soke Dokar Da Ta Buƙaci Sai Ɗalibi Ya Kai Shekaru 18 Kafin Shiga Jami’a A Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sabon ministan Ilimi, Olatunji Alausa, ya soke dokar da ta buƙaci sai ɗalibi ya kai shekaru 18 kafin shiga jami’a wanda tsohon ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya kawo.
Minista Alausa ne ya bayyana wannan mataki a yayin da jawabi bayan shiga ofishinsa a matsayin sabon ministan Ilimi a ranar Talata.
Cin Fuska Ne A Wajena Yadda Ake Faɗin “Abba Tsaya Da Ƙafar Ka” – Gwamnan Kano
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ne ya naɗa shi bayan cire tsohon ministan ilimi Tahir Mamman sakamakon sake fasalin ministocinsa.
Sannan shugaba Tinubu ya sauya wa ƙaramin ministan ilimi, Yusuf Sununu, ma’aikata zuwa ma’aikatar hukumar jin-ƙai da yaƙi da talauci.
DOKAR CIKA SHEKARU 18 DA TAHIR MAMMAN YA KAWO
A makon da ya gabata ne aka cire Tahir Mamman daga kujerarsa wanda kafin sannan ne ya umarci hukumar shirya jarrabawa ta ƙasa (JAMB) da kuma manyan makarantu a Najeriya kan ka da su ba wa kowanne ɗalibi da bai kai shekaru 18 ba gurbin karatu.
Ya ba da wannan umarni ne a lokacin da yake jawabi a wurin taron tattauna tsare-tsaren hukumar JAMB tare da shugabannin manyan makarantun game da shirin ba wa yara gurbin karatu na shekarar 2024/2025.
Tsohon ministan ya bayyana ewa wannan mataki ba son ransa ba, abin da ya dace a yi da ya shafi tsare-tsaren hukumar.
Ya ce, “dokokinmu sun tanadi cewa lallai ne yaro ya yi shekaru 6 a firamare – haka ne duk da akwai yaran da suke shafe shekaru biyar. Baya ga firamare, akwai ƙaramar sakandare shekara uku da kuma babban sakandare shekara uku. Wannan ba ya buƙatar sahalewar minista, wannan abu ne da muke da shi a dokance.
SABON MINISTAN ILIMI YA YI SAUYA WANNAN DOKA
Sabon ministan Ilimi ya soke wannan ƙuduri wanda ya ce shekarun da aka amince ɗalibi ya shiga manyan makarantu su ne 16. Sannan za a iya buɗe ƙofa ga yara ‘yan baiwa.
Ya ce shekaru 18 zai iya zama barazana ga shirin gwamnatin tarayya na rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a faɗin ƙasar nan.
Sannan ya ce gwamnatin tarayya na da burin ciyar da ilimi gaba ta hanyar yin aiki a aikace ba rubuce ba musamman a manyan makarantun Najeriya.
Alausa ya ce ilimin da mutum zai iya sarrafawa shi ne tsarin zai magance rashin aikin yi a Najeriya da zai tallafa musu wajen samun abun yi.
Ministan Ilimin ya ce za su yi aiki da kamfanoni masu zaman kansu wajen horas da ɗalibai domin kai wa ga gaci.