Politics
Dan Majalisar Jihar Kano Ya Sauya Sheka Daga NNPP Zuwa APC

Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Sumaila, Hon. Zubairu Hamza Masu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Hon. Masu ya bayyana hakan ne a cikin wata wasikar murabus da ya aike wa Shugaban Majalisar, Rt. Hon. Ismail Falgore, wadda aka karanta a zaman majalisa na yau.
A cikin wasikar, Hon. Masu ya bayyana rikice-rikicen cikin gida da ke damun jam’iyyar NNPP, musamman rikicin shugabanci da kararraki a kotu, a matsayin manyan dalilan da suka sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar.
Ya bayyana cewa akwai rikice-rikice na shugabanci a matakin jiha da na kasa, inda ya ambaci Dr. Suleiman Hashim Dungurawa da Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa a matakin jiha, da kuma Dr. Ahmed Ajuji da Dr. Agbo Major a matakin kasa.
Sauya shekar Hon. Masu zai fara aiki daga ranar 12 ga Mayu, 2025, kuma ya sha alwashin ba da cikakken goyon bayansa ga jam’iyyar APC a dukkan matakai.