Connect with us

News

NUJ Kano Ta Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Ɗan Jarida Adamu Ibrahim Getso ‎

Published

on

NUJ Logo (1)

Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Reshen Jihar Kano, ta bayyana alhini da jimami kan rasuwar fitaccen ɗan jarida kuma gogaggen shugaban kafafen yaɗa labarai, marigayi Alhaji Adamu Ibrahim Getso.

‎A cikin wata sanarwa da Sakatariyar ƙungiyar, Hauwa Suleiman Zahradeen, ta fitar kuma ta rabawa manema labarai, Shugaban NUJ na Kano mai riƙon ƙwarya, Kwamared Mustapha Gambo, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa da kuma al’ummar garin Getso da ke Ƙaramar Hukumar Gwarzo bisa wannan babban rashi.

Advertisement

NUJ Kano Ta Yi Alhinin Rasuwar Fitaccen Ɗan Jarida Adamu Ibrahim Getso ‎

‎Ya bayyana rasuwar marigayin a matsayin babban gibi ga harkar yaɗa labarai a Kano da Najeriya baki ɗaya, yana mai cewa gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa aikin jarida da wayar da kan jama’a za ta ci gaba da kasancewa abin koyi ga masu tasowa a fannin.

Advertisement

‎“Marigayi Adamu Ibrahim Getso ƙwararren ɗan jarida ne kuma gogaggen mai gudanar da harkokin yaɗa labarai wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen yi wa al’umma da sana’ar jarida hidima. Tasirin da ya yi wajen wayar da kan jama’a da yaɗa sahihan bayanai zai kasance abin tunawa na tsawon lokaci,” in ji Gambo.

‎Sanarwar ta kuma yi nuni da muhimmiyar rawar da marigayin ya taka a matsayinsa na babban mai gabatar da shirye-shiryen siyasa da ci gaba a lokutan mulkin tsohon gwamnan Kano, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, a wa’adinsa na farko da na biyu.

Advertisement

‎NUJ ta ce ta hanyar ƙwarewarsa a harkar watsa shirye-shirye, marigayin ya taimaka matuƙa wajen sanar da jama’a, ilimantar da su da kuma ƙarfafa fahimtarsu kan manufofi da ayyukan gwamnati da kuma muhimman al’amuran da suka shafi al’umma a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

‎Ƙungiyar ta bayyana cewa za ta ci gaba da tuna marigayin a matsayin jajirtaccen ƙwararren ɗan jarida wanda ya bar tarihi mai ɗorewa a harkar yaɗa labarai.

Advertisement

‎NUJ Kano ta kuma yi addu’ar Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya ba iyalansa da masoyansa haƙurin jure wannan rashi, tare da sanya shi a Aljannatul Firdaus.

‎Rasuwar Adamu Ibrahim Getso ta girgiza al’ummar kafafen yaɗa labarai a Kano, inda abokan aikinsa da masu bibiyar shirye-shiryensa ke ci gaba da bayyana alhininsu kan wannan babban rashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending