News
Buratai Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Harin Boko Haram A Borno

Tsohon Hafsan Sojojin Kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai (mai ritaya), ya tsallake rijiya da baya a ranar Juma’a, bayan da motocin da ke dauke da shi da rakiyarsa suka gamu da harin bindiga daga ‘yan ta’addan Boko Haram a jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ta’addan ne suka kitsa harin a kusa da wata sansanin soja da ke yankin gaba da fagen fama, inda suka bude wuta kan tawagar da ke tare da tsohon hafsan.

Boko Haram Sun Farmaki Tsohon Hafsan Sojojin Æasa Buratai A Borno.

Sanata mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ne ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Television a daren Lahadi.

A cewarsa, harin ya kara dagula lamarin tsaro a yankin Arewa maso Gabas, wanda ke ci gaba da fama da hare-haren Boko Haram da na ‘yan ISWAP.
Advertisement

Ndume ya ce dakarun da ke rakiya Buratai sun mayar da martani cikin jarumta, inda suka shiga musayar wuta da ‘yan ta’addan, duk da cewa an samu barna a bangaren kayan aiki.

“Muna cikin wani mawuyacin hali na tsaro. Kwanaki biyu da suka gabata, an kai hari kan Laftanar Janar Buratai a kusa da wani sansanin soja da ke gaba da fagen fama. Sai dai dakarunsa sun nuna jarumta wajen dakile harin, kodayake ‘yan ta’addan sun lalata kayayyakin yaki da dama,” in ji Ndume.

Sai dai har zuwa yanzu babu rahoton asarar rai da aka tabbatar a harin.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara fuskantar kalubale na tabarbarewar tsaro a wasu yankunan Arewa maso Gabas, lamarin da ke kara sanya damuwa cikin zukatan al’ummar yankin.
Advertisement