Connect with us

Politics

Tsofaffin Ƙansilolin Jihar Kano Sun Yi Mubaya’a ga Shugaban Riƙo na NNPP na Jihar Kano Hon. Abdullahi Zubairu Abiya

Published

on

1767543102968
Spread the love

Tsofaffin Ƙansilolin kananan hukumomi daga sassa daban-daban na Jihar Kano sun bayyana cikakken goyon bayansu tare da yin mubaya’a ga Shugaban Riƙo na Jam’iyyar NNPP a Jihar Kano, Hon. Abdullahi Zubairu Abiya, a wani taro na musamman da suka gudanar a Kano.

A yayin taron, tsofaffin ƙansilolin sun jaddada cewa sun yanke wannan shawara ne bisa la’akari da irin kwarewa, jajircewa da kuma tsayayyen hangen nesa da Hon. Abdullahi Zubairu Abiya ke da shi wajen tafiyar da al’amuran jam’iyya da kuma ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai a faɗin jihar.

 

Sun bayyana cewa goyon bayan da suka nuna wata alama ce ta amincewa da shugabancinsa, tare da ƙudurin ba shi cikakken haɗin kai domin tabbatar da bunƙasar jam’iyyar NNPP daga matakin ƙananan hukumomi zuwa matakin jiha.

Advertisement

A jawabinsa, Hon. Abdullahi Zubairu Abiya ya gode wa tsofaffin ƙansilolin bisa wannan mubaya’a, inda ya bayyana cewa goyon bayansu zai ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da aiki tuƙuru domin haɗa kan ‘ya’yan jam’iyya, tabbatar da adalci, gaskiya da kuma bin dokoki da ƙa’idojin jam’iyyar.

 

Haka kuma, tsofaffin ƙansilolin sun yi kira ga al’ummar Jihar Kano da dukkan mambobin jam’iyyar NNPP da su mara wa shugabancin Hon. Abdullahi Zubairu Abiya baya, domin cimma manufofin ci gaba, zaman lafiya da nasarorin jam’iyyar a nan gaba.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *