Connect with us

Business

An Shigo Da Man Fetur Na Sama Da Naira Tirliyan 12 A Cikin Najeriya

Published

on

Spread the love

Yayin da Najeriya ke cigaba da ƙoƙarin haɓaka aikin tace man fetur a cikin gida, bayanan da hukumar kula da harkokin sarrafawa, sayarwa da rarraba man fetur ta fitar sun nuna cewa an shigo da man fetur da darajarsa ta kai Naira tiriliyan 12.8 a cikin kasar daga watan Agusta 2024 zuwa Oktoba 2025.

An cimma wannan adadi ne ta wajen amfani da yadda man fetur ke isa ƙasar akan farashin Naira 829.77 a kowace lita, kuma an kai ga wannan lissafin ne ta wajen haɗa yawan lita-lita na man da aka ce an shigo da su a duk rana, wanda ya kai lita biliyan 15,435,000,000.

Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Sanadiyyar Banka wa Kauye Wuta A Jigawa 

Bayanai sun nuna cewa an fi shigo da man fetur ne a watan Satumba na 2024 lokacin da ba a iya samar da shi a cikin gida, inda aka shigo da lita biliyan 1.52; sai watan Agusta 2024 da aka shigo da lita biliyan 1.38; sai kuma Disamba 2024 da lita biliyan 1.31.

A watan Oktoba na 2025, an shigo da lita biliyan 1.17 na man fetur, sannan lita biliyan 1.12 a watan Nuwamba. Amma a watan Janairu na 2025, adadin ya ragu matuka zuwa lita miliyan 765.7, sai ya ɗan ƙaru zuwa lita miliyan 770 a watan Fabrairu da lita miliyan 889.7 a watan Maris.

Advertisement

A ɗaya bangaren, man fetur da ake samarwa a cikin gida ya kai lita biliyan 7,208,280,000 kuma duk daga matatar Dangote aka samar da su.

 

 

FRI HAUSA 

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *