Connect with us

Business

Najeriya Ta Samu Rarar Naira Triliyan 12.60 a Cinikayyar Kasa Da Kasa A Zango Na Biyu Na 2026

Published

on

Shipping containers 1

Rarar da Nijeriya ta samu a cinikin kayayyaki da ƙasashen waje ta haura naira tiriliyan 12.60 a zango na biyu na shekarar 2026, fiye da ninki biyu na abin da aka samu a daidai wannan lokaci na shekarar 2025.

Ƙididdigar ta nuna cewa fitar da kayayyaki daga Nijeriya ya ƙaru, yayin da shigo da kayayyaki ya ragu idan aka kwatanta da zango na biyu na shekarar da ta gabata.

Na Siyar Da Tagwayen Jarirai  Maza Kan Naira Dubu 300 — Wacce Ake Zargi

Hukumar Kididdiga ta Ƙasar, NBS ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta kan ƙididdigar cinikin kayayyaki da ƙasashen waje na zango na biyu na 2026.

A cewar rahoton, ribar cinikin kayayyakin Nijeriya ta kai naira biliyan 12,596.86, wanda ke wakiltar ƙarin kashi 101.32 cikin 100 idan aka kwatanta da zango na biyu na 2025.

Rahoton ya kuma nuna cewa jimillar cinikin kayayyakin Nijeriya ta kai naira tiriliyan 41.44 a zango na biyu na 2026.

Advertisement

Wannan ya nuna ƙarin kashi 5.61 cikin 100 daga naira tiriliyan 39.24 da aka samu a zango na biyu na 2025, da kuma ƙarin kashi 19.13 cikin 100 daga naira tiriliyan 34.79 da aka samu a zangon farko na 2026.

A gefe guda, fitar da kayayyaki daga Nijeriya ya ƙaru zuwa naira tiriliyan 27.02 a zango na biyu na 2026, daga naira tiriliyan 22.75 a daidai wannan lokaci na shekarar 2025, wanda ke wakiltar ƙarin kashi 18.77 cikin 100.

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending