Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Hallaka ’Yan Ta’adda 8, Sun Ceto Mutanen Da Aka Yi Garkuwa Da Su

Published

on

militaryarmy 1000x600
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Dakarun Operation FANSAN YAMMA sun hallaka wasu da ake zargin ’yan ta’adda ne guda takwas, tare da ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara.

Haka kuma, sojojin sun ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda ɗaya, bindigogi ƙirar gida guda uku, babura uku, adduna da wasu layu.

Harry Kane Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or 2026

Jami’in yaɗa labarai na rundunar, Kyaftin Tamuno Sinivie, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

A Jihar Katsina, sojojin sun kashe mutane biyu da ake zargin ’yan ta’adda ne yayin musayar wuta a Ƙaramar Hukumar Sabuwa, ranar Asabar, 24 ga Oktoba.

A yayin samamen, sun ceto wani mutum mai suna Suleiman Umar, mai shekaru 42, wanda aka yi garkuwa da shi, tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 da babur guda ɗaya.

Advertisement

A Jihar Kaduna kuwa, sojoji tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai na Civilian Joint Task Force sun kashe wasu mutane shida da ake zargin ’yan ta’adda ne bayan sun dakile wani harin kwanton ɓauna a Ƙaramar Hukumar Igabi.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa waɗanda ake zargin sun yi awon gaba da wasu mutane biyu a wani hari da suka kai a baya.

A Jihar Zamfara, sojojin sun ceto mutane biyu, Shehu Chete, mai shekaru 40, da Bugu Bedi, mai shekaru 25, a garin Bagega da ke Ƙaramar Hukumar Anka, ranar Lahadi, 25 ga Oktoba.

Sanarwar ta ce an kai mutanen asibiti domin duba lafiyarsu kafin daga bisani a miƙa su ga iyalansu.

Kyaftin Sinivie ya bayyana cewa sojojin na ci gaba da gudanar da sintiri da bincike domin cafke waɗanda suka tsere, ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da dakile ƙarin hare-hare.

Ya kuma buƙaci mazauna yankunan da abin ya shafa da su riƙa bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai game da duk wani abu da suke zargi, domin taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

Advertisement

 

 

 

LEADERSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending