Connect with us

News

Kotu Ta Umurci El-Rufai Ya Kare Kansa Kan Zargin Sauraron Wayar Nuhu Ribadu

Published

on

El Rufai court 1000x600 (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta umarci tsohon Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai da ya gabatar da kariyarsa a shari’ar da ake yi masa kan zargin saurarar wayar mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro malam Nuhu Ribadu ba bisa ƙa’ida ba.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta bayar da umarnin a ranar litinin bayan ta yi watsi da buƙatar El-Rufai na neman kotu ta dakatar da shari’ar saboda a cewarsa masu gabatar da ƙara ba su gabatar da isassun hujjoji a kansa ba.

Dakarun Sojin Sama Sun Yi Amfani Da Kusan Litar Man Jirgi Miliyan 10 Wajen Gudanar Da Ayyukan Tsaro

Mai Shari’ar ta bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun gabatar da isassun hujjojin da suka sa ya zama dole El-Rufai ya amsa zarge-zargen da ake yi masa.

El-Rufai ya shigar da buƙatar ne bayan hukumar DSS wadda ke tuhumarsa ta kammala gabatar da shaidu biyu a gaban kotu.

Lauyan tsohon gwamnan, Paul Erokoro, ya roƙi kotun da ta wanke shi, yana mai cewa hujjojin da masu gabatar da ƙara suka gabatar ba su isa a tilasta wa wanda yake karewa ya gabatar da kariyarsa ba.

Advertisement

Sai dai lauyan DSS, Oluwole Aladedoye, ya buƙaci kotun ta yi watsi da buƙatar, tare da umartar El-Rufai ya kare kansa kan zarge-zargen.

Shari’ar ta samo asali ne daga kalaman da El-Rufai ya yi a wata hira da gidan talabijin na Arise TV a watan Fabrairun 2026, inda ya yi zargin cewa an saurari tattaunawar wayar Ribadu, sannan aka ba shi damar jin abin da aka tattauna.

DSS na tuhumarsa bisa zargin sa hannun da ake dangantawa da saurarar tattaunawar wayar ba bisa ƙa’ida ba. Sai dai zarge-zargen na nan a gaban kotu, kuma hukuncin da aka yanke a wannan mataki ba yana nufin an tabbatar da laifinsa ba.

Kotun ta ɗage ci gaba da shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, 2026, domin El-Rufai ya gabatar da kariyarsa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending