Connect with us

Opinion

TSARIN KAURAN GWANDU: Yadda Malami Ke Doke Sauran Gwamnoni a Fadin Najeriya

Published

on

Nasiru Idris

Daga Abba Anwar

Ba maganar hayaniyar ayarin motoci masu duhun gilashi ba ne kokarin gwamnati. Ba a cikin hayaniya ake gane aikin gwamnati ba. Aikin gwamnati yana cikin shin ma’aikacin da ya yi ritaya bayan shekaru 35 yana aiki zai iya karbar gratuity dinsa bayan jiran shekaru 10? Shin mace mai juna biyu a Argungu za ta samu magani da ungozoma da karfe 2 na dare? Shin jihar da ta bar azuzuwanta su zama kango yanzu tana cika alkawura? Ta nan ne ake gane gwamnan da zai dore.

A cikin shekaru biyu da suka wuce, aiki ya kai ni sassan Najeriya – daga Minna zuwa Maiduguri, daga Birnin Kebbi zuwa Makurdi, daga Legas zuwa Owerri da Asaba. Labarin iri daya ne a wurare da yawa. A na gina manyan gadoji, amma bukatun talaka na yau da kullum suna durkushewa. Jihohi da yawa suna gina abin kallo. Kadan ne ke gina dan Adam.

Gwamnatin Kebbi Ta Amince Da Biyan N75,000 A Matsayin Karin Albashi Ga Malamai 17,620

A Jihar Kebbi, Kwamared Dr. Nasir Idris, Kauran Gwandu, ya zabi na biyun. Kuma shi ya sa yau, idan ka ajiye takardar ayyukansa kusa da na takwarorinsa da yawa, ya fita daban. Bari na yi bayani.

Lokacin da Nasir Idris ya karbi mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, a na bin Kebbi bashin gratuity tun daga 2015. Katafaren sakatariyar da aka fara a 2006 ta zama kango a Gwadangaji inda macizai ke zaune. Titunan cikin garin Birnin Kebbi, Argungu da Yauri duk sun lalace. Makarantu sama da 1,000 sun lalace. Asibitocin PHC ba su da ma’aikata.

Advertisement

Bayan shekaru uku, an samu cigaba a ko’ina har ma abokan hamayyarsa ba za sa iya musa ba. Kawai mai karatu ya karanta yadda abubuwan suke kamar yadda na zayyano su a kasa.

A bangaren Ilimi an gyara makarantu sama da 2,000 an kuma sanya musu kayan aji, an gina sabbin makarantu sama da 200 tun daga tushe. An dauki malaman firamare 2,000, na sakandare 1,500, na kimiyya 500, an kuma mayar da malaman agaji 300 aiki na dindindin. Ya soke aikin wucin-gadi (casual). A baya a Kebbi malami kan yi aiki shekaru 10 akan N15,000 a matsayin dan kwantaragi. Yanzu an bashi aiki na dindindin.

Ya dawo da alawus din shugabannin makaranta da aka bari shekaru 20 da suka wuce. Ya biya bashin tallafin karatu na Naira Bilyan Shida da Miliyan Dari Biyu (N6.2b) da ya gada. Ya dauki nauyin dalibai 23,558, da kuma wasu 144 a India da Masar. Ya kara kudin ciyar da daliban kwana zuwa N300 miliyan duk wata. Ya sanya hannu kan dokar tsawaita shekarun ritayar malami zuwa 65. Babu wata jiha a Najeriya da ta taba yin wannan kwallin.

A bangaren Lafiya ya farfado da Manyan Asibitoci 22, PHCs 179 da kantunan magani 63. Ya dauki ma’aikatan lafiya sama da 2,200. Ya tura asibitocin mota zuwa yankunan kogin Argungu da Yauri.

Ya yi kokari matuka don ganin Kebbi ba ta kasance a baya ba a ci gaban ababen more rayuwa. Ya gina da fadada tituna sama da 88, ciki har da muhimmiyar hanyar Koko-Zuru-Mahuta-Dabai mai tsawon kilomita 87 da aka dawo da ita da N64 biliyan bayan shekaru 15 da aka yi watsi da ita. Sama da kilomita 300 na titunan karkara da suka hada al’ummar manoma 150. Ya gina sabuwar Sakateriya, Tashar Mota ta Central, ya sake gina Kasuwar Kayan Gwari.

A matsayinsa na jagora mai kishin al’umma wanda ya yi imani da inganta sufurin jama’a don saukaka zirga-zirga, ya samar da manyan motocin sufuri sama da 800 a kananan hukumomi 21, da kuma motocin dukkan manyan makarantun jihar. Dalibi a Zuru yanzu yana biyan N100 maimakon N500 na achaba.

Advertisement

A matsayinsa na dan kungiyar kwadago yana baiwa walwalar ma’aikata fifiko. Yana biyan mafi karancin albashi N75,000 alhali na tarayya N70,000 ne. Yana cikin gwamnoni uku na farko da suka fara biya. Ya biya bashin gratuity da alawus din mutuwa sama da N10 biliyan, ciki har da N2.11 biliyan na masu ritaya 772 a kwanan nan. Babu jingine. Ana biyan albashi 24 zuwa 25 ga kowane wata. Ya tsawaita shekarun aiki na malaman makaranta, ma’aikatan lafiya da na dabbobi.

A bangaren Noma ya raba taki buhu mota 500 kyauta, famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana 10,000, famfo 10,000 masu amfani da gas, kekunan noma da feshi. Ya samo tallafi daga Bankin Raya Afirka (AfDB) don gina babban yankin sarrafa kayan noma a Argungu. Ya kaddamar da Kaura Cares – tallafin rayuwa na biliyoyin Naira ga mata da matasa.

Don tsaron al’ummarsa ya bayar da motoci Hilux sama da 100 da babura kusan 7,000 ga jami’an tsaro da ‘yan banga, wanda ya sa ‘yan gudun hijira a Danko Wasagu suka koma gida cikin farin ciki.

Alhazan Jihar Kebbi na daga cikin alhazan da suka fi samun kulawa mai kyau daga gwamnatocin jihohi a fadin kasar. Tsari da gudanar da hukumar alhazai a Jihar Kebbi, ya nuna sarai yadda Gwamnan yake da rikon addini. Haka ma shugabannin hukumar da ke gudanar da al’amuranta. Haka abin yake a sauran ma’aikatu da hukumomi.

Nasa ne yafi kyau.

Mai karatu zai iya fahimtar Mai Girma Gwamna sarai, idan aka kwatanta shi da sauran gwamnoni a fadin kasar. Yanzu, a kwatanta shi da gwamnoni biyu daga kowane shiyya. Ba don a yi izgili ba, sai don a nuna inda Kebbi ke kan gaba.

Advertisement

A Arewa ta Tsakiya, a Jihar Neja ta Umar Bago da Jihar Benue ta Hyacinth Alia, an yarda cewa dukkansu masu aiki ne. Bago na kokari a fannin noma da sabunta birnin Minna. Alia na kokarin biyan bashin albashi. Amma Kebbi ta fi su a abu daya: daidaito wajen biya. A lokacin da Neja da Benue ke ta tattaunawa kan aiwatar da N70k a karshen 2024 suna fama da tarin bashin gratuity, Kebbi ta riga ta biya N75k kuma ta biya sama da N10b na gratuity. A ilimi, yayin da Neja ta gyara makarantu kusan 400, Kebbi ta gyara sama da 2,000. A titunan karkara, titin kilomita 300 na Kebbi da ya hada al’ummomi 150 ya fi na jihohin Arewa ta Tsakiya da yawa inda titunan karkara har yanzu na masu tallafi ne.

A Arewa maso Gabas, a Jihar Borno ta Babagana Zulum da Jihar Bauchi ta Bala Mohammed, an yarda cewa Zulum gwarzo ne. Babu wanda ya musanta hakan. Amma har Zulum ya yarda cewa walwala har yanzu kalubale ne saboda matsalar yan tayar da kayar baya. Kebbi, da ke da zaman lafiya, ta iya abin da Borno ba ta iya ba tukuna – cikakken dawo da CONHESS, albashin N75k, da mayar da malaman kwantaragin aiki na dindindin. Bauchi ta yi kokari a ababen more rayuwa a cikin birnin Bauchi, amma har yanzu tana fama da makarantu sama da 1,500 marasa kyau da jinkirin albashi a kananan hukumomi. Kebbi ta gyara makarantu fiye da Bauchi a cikin lokaci guda kuma tana biyan albashi da wuri.

A Arewa maso Yamma, a Jihar Sakkwato ta Ahmed Aliyu da Jihar Zamfara ta Dauda Lawal, makwaftan juna ne, amma anan ne bambancin ya fi bayyana. Wani rahoton kasa na baya-bayan nan kan aikin PHC ya sanya Zamfara a matsayin jiha mafi kasa a aikin PHC, sai Sakkwato, Katsina, makwabtan Kebbi a matsayin masu rauni. A wasu daga cikin wadancan jihohin, kasafin kudin PHC ya yi daga 0 zuwa 6.5% – ma’ana kudin da a ka yi kasafi ba a saki ba. A Sakkwato, har yanzu akwai rahotannin manyan asibitoci da aka yi watsi da su na Miliyoyin Naira yayin da mutane ke tafiya nesa. A Zamfara, bashin albashi da fansho babban lamari ne. Kebbi, makwabciyarsu, ta farfado da PHCs 179, ta dauki ma’aikatan lafiya 2,200, kuma ba ta bin bashin gratuity ko sisi. Yayin da Zamfara da Sakkwato ke kokawa don samar da auduga a asibiti, Kebbi tana gina Cibiyar Cancer, ICU, da motoci 800. Shiyya daya, kason kudi daya, amma sakamako daban.

A Kudu maso Yamma, a Jihar Legas ta Babajide Sanwo-Olu da Jihar Oyo ta Seyi Makinde kwatancen ya tafi haka. Legas na da kudi – kasafin N2.2 tiriliyan. Ta na yin Blue Line, Red Line, tashar Lekki. Amma a duba walwalar ma’aikata. Legas har yanzu tana biyan N70k kuma tana da bashin fansho. Kebbi tana biyan N75k. A ilimi, Legas na da makarantun gwamnati 1,700, da yawa har yanzu cunkushe da dalibai 80 a aji daya. Kebbi ta gyara makarantu 2,000 – fiye da yawan makarantun gwamnati a Legas. Oyo ta yi kokari da titin 5km a kowace karamar hukuma da kari na albashi, amma har yanzu tana da makarantu 700 da ke bukatar gyara kuma tana tattaunawa kan biyan gratuity daga 2013. Kebbi ta biya duka daga 2015 zuwa yau. Ba wai Legas ba ta aiki ba. Sai dai Kebbi da kashi daya cikin goma na kason Legas ta yi abin da ya fi yawa ga malamai da masu ritaya.

A Kudu maso Gabas, a Jihar Anambra ta Chukwuma Soludo da Jihar Imo ta Hope Uzodimma, ga kwatancen. Soludo masanin tattalin arziki ne, kwararre a gyaran kudi, amma Anambra ta samu zanga-zangar malamai kan aikin kwangila da karancin albashi.

Imo ta samu matsala wajen daidaiton albashi da fansho. Kebbi ta soke aikin kwangila gaba daya, ta ba da takardun aiki na dindindin, ta dawo da alawus da aka bari shekaru 20. Yayin da Anambra da Imo ke fama da zaman gida na IPOB da ke shafar kalandar makaranta, Kebbi ta kara ciyar da makaranta zuwa N300m duk wata kuma ta ci gaba da bude makarantu. A ababen more rayuwa, yayin da Kudu maso Gabas ke mai da hankali kan gadoji a Owerri da Awka, Kebbi ta mai da hankali kan titunan karkara na kilomita 300 da ke kai shinkafa kasuwa – wanda ya taba GDP kai tsaye.

Advertisement

A Kudu maso Kudu, a Jihar Rivers karkashin Sim Fubara da Jihar Delta karkashin Sheriff Oborevwori, duka suna da kason FAAC mai yawa saboda mai. Kasafin Ribas ya haura N800bn, Delta ma haka. Suna gina manyan gadoji. Amma a duba alamun zamantakewa: Ribas har yanzu tana bin bashin gratuity daga 2015, Delta tana da makarantu 2,000 da ke bukatar gyara a cewar rahoton SUBEB dinta.

Kebbi, da kasafin kusan N300bn, ta biya gratuity, ta gyara makarantu 2,000, kuma ta gina tituna 88. Bankin Duniya na ci gaba da cewa: babban ababen more rayuwa ba tare da jari na dan Adam ba baya rage talauci. Kebbi ta zabi jari na dan Adam da farko – malamai, ma’aikatan lafiya, taki, motoci – kuma shi ya sa Sarkin Musulmi ya ce “Ban taba ganin wata jiha inda gwamna ya hada dukkan gwamnoninsa da su ka shude kamar yadda Nasir Idris ya yi ba.” A Rivers da Delta, tsofaffin gwamnoni suna kotu da gwamnoni na yanzu. A Kebbi, Aliero, Dakingari da Bagudu suna zaune a teburi daya.

Me ya sa wa’adi na biyu ba maganar muhawara ba ne. Idan aka duba ci gaban da ya kawo a jihar, da kwatanta shi da sauran jihohi a fadin shiyyoyi shida za mu iya cewa neman a sake zabensa ba abin a tsaya a na musu a kai ba ne. Shi ya sa Sarkin Argungu ya taba cewa “Ya cancanci wa’adi na biyu. Lokacinsa ne.” Shi ya sa shugabannin APC na kasa suka taba lissafa shi cikin gwamnoni uku mafi fice na APC. Shi ya sa tsohon Gwamna Aliero, wanda yake a PDP, ya furta, “Na ga abubuwan ci gaba da aka yaba, amma fargabata ita ce jam’iyyata na iya shiga matsala da irin gudu da kake yi.”

Wa’adi na biyu ba na jam’iyya ba ne. Na cigaba ne. Hanyar Koko-Zuru na bukatar shekaru 8. Yankin sarrafa kayan noma na Argungu na bukatar shekaru 8. Titunan karkara na kilomita 300 na bukatar shekaru 8. Ya zama ga masu zabe su dage su tabbatar ya sake dawowa a wa’adi na biyu. Idan su ka yi haka to sun nemawa kansu cigaba mai alheri.

Gwamnonin da ke gina wasu abubuwa suna samun hoto. Gwamnonin da ke gina malamai, masu ritaya, PHCs da titunan karkara suna samun kuri’a. Kuma suna samun gado.

Nasir Idris na cikin rukuni na biyu. Kuma shi ya sa, idan ka ajiye shi kusa da takwarorinsa da yawa a fadin shiyyoyi shida, bambancinsu ya na da yawa. Yana cikin ajin da yaro yanzu ke zaune a kan sabon kujera, a cikin PHC inda mace yanzu ta ga ungozoma, da kuma cikin sakon banki da ke shiga a ranar 25 ga kowane wata.

Advertisement

Da irin nasarorin da aka samu a Jihar Kebbi karkashin gwamnatin Kauran Gwandu, ruhin sabon bege ya tashi a zukatan masu zabe don baiwa dukkan ‘yan takarar APC tun daga sama har kasa dukkan goyon bayan da ake bukata don sake zabe.

Tsarin Kauran Gwandu shine cigaba na ainihi. Wanda ba za a iya kau da kai ba dole a na bukatar mara masa baya. 

 

Anwar ya rubuta daga Kano

Talata, 13 ga Oktoba, 2026

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending