Connect with us

Sports

Ƙungiyar Masoyan Bayern Munich Ta Kano Ta Taya Harry Kane Murnar Lashe Ballon d’Or 2026

Published

on

IMG 20261027 WA0011
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Ƙungiyar masoyan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bayern Munich da ke Jihar Kano, ta taya ɗan wasan ƙungiyar, Harry Kane, murnar nasarar da  ya samu ta lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2026.

Shugaban ƙungiyar ta Kano, Mujtaba Bature Marmara, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya ce nasarar Kane abin alfahari ce ga masoyan Bayern Munich a Kano, Nijeriya da sauran sassan duniya.

Uwar Gidan Gwamnan Kebbi Ta Jagoranci Gangamin Wayar Da Kai Kan Cutar Daji, Ta Ba Matan ’Yan Kasuwa Tallafin Naira Miliyan 20

Sanarwar ta bayyana cewa nasarar ta nuna ƙwarewar ɗan wasan, jajircewarsa da kuma yadda yake taka rawar gani a fagen ƙwallon ƙafa.

A cewar Marmara, bajintar Kane, musamman wajen zura ƙwallaye da taimaka wa ƙungiyarsa samun nasarori, ta sa masoyan Bayern Munich ke da kyakkyawan fata game da makomar ƙungiyar.

“Mun yi matuƙar farin ciki da wannan gagarumar nasara ta Harry Kane. Jajircewarsa da ƙoƙarinsa na neman ɗaukaka sun ci gaba da zaburar da mu a matsayin masoyan Bayern Munich.

Advertisement

“Wannan karramawa abin alfahari ne ga ƙungiyarmu da masoyanta, kuma muna fatan za ta ƙara ɗaukaka tarihin Bayern Munich tare da zaburar da sauran ’yan wasa wajen neman nasara,” in ji sanarwar.

Ya ƙara da cewa Kane ya taimaka wajen ƙara wa tarihin Bayern Munich armashi tun bayan komawarsa ƙungiyar, yana mai cewa nasarar ta ƙara nuna ingancin ’yan wasan da kuma burin ƙungiyar na ci gaba da yin fice a gasannin cikin gida da na ƙasashen duniya.

Marmara ya kuma taya shugabannin ƙungiyar, masu horaswa, ’yan wasa da sauran masoyan Bayern Munich murna bisa ƙoƙarinsu na ci gaba da ɗaukaka martabar ƙungiyar.

Ya ce nasarar Kane ba ta tsaya ga shi kaɗai ba, domin za ta zama abin koyi ga matasa masu sha’awar ƙwallon ƙafa waɗanda ke burin kaiwa matsayi mafi girma a harkar.

 

Za a shirya bikin murnar nasarar

Advertisement

 

Shugaban ya bayyana cewa ƙungiyar masoyan Bayern Munich ta Jihar Kano na shirin shirya wani biki domin murnar nasarar Kane.

Ya ce bikin zai haɗa mambobin ƙungiyar da sauran masoya ƙwallon ƙafa, domin ƙarfafa zumunci da haɗin kai a tsakaninsu.

A cewarsa, bikin zai kuma zama wata dama ta yaɗa kyawawan ɗabi’un wasanni, haɗin kai da zaman lafiya ta hanyar ƙwallon ƙafa.

Marmara ya yi kira ga masoyan Bayern Munich da ke Jihar Kano da su kasance masu haɗin kai tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa ƙungiyar.

Ya kuma buƙaci masoyan da ba su yi rajista da reshen ƙungiyar na Kano ba da su yi rajista, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙar mambobi da inganta ayyukan ƙungiyar.

Advertisement

Ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da faɗaɗa mambobinta tare da yaɗa kyawawan manufofin Bayern Munich a tsakanin masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Kano da Nijeriya baki ɗaya.

Domin yin rajista ko samun ƙarin bayani, sanarwar ta buƙaci masu sha’awar shiga ƙungiyar da su tuntubi Shugaban ƙungiyar, Mujtaba Bature Marmara, ta lambar waya 0803 630 6968.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending