Connect with us

Entertainment

Burna Boy Da Shakira Za Su Yi Waƙa Yayin Hutun Rabin Lokaci A Wasan Ƙarshe Na Kofin Duniya

Published

on

IMG 3194 768x663 1

Shahararren mawaƙin Najeriya kuma wanda ya lashe kyautar Grammy, Burna Boy, tare da fitacciyar mawaƙiyar ƙasar Kolombiya, Shakira, za su jagoranci nishaɗantar da masu kallo a hutun rabin lokaci na wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya ta 2026.

A wani bidiyo da Burna Boy ya wallafa a shafinsa na X, an ga yadda shi da Shakira suka haɗu cikin annashuwa yayin shirye-shiryen gabatar da wasan kwaikwayon da za a yi a gaban miliyoyin masu kallo daga sassan duniya.

Gashash Ya Bukaci Gwamnan Abba Da Gwarzo Su Yi Siyasar Girmamawa Maimakon Cin Mutuncin Juna Don Zaman Lafiya Da Kimar  Kano

Burna Boy ya bayyana farin cikinsa da samun damar hawa babban dandali tare da Shakira, yana mai cewa hakan wata babbar dama ce ta nuna al’adun Afirka a ɗaya daga cikin manyan bukukuwan wasanni na duniya.

Hukumar FIFA ta riga ta tabbatar da cewa Burna Boy da Shakira ne za su jagoranci shirin nishaɗin hutun rabin lokaci na wasan ƙarshe, tare da wasu fitattun taurarin waƙa na duniya.

Daga cikin waɗanda za su halarci shirin akwai BTS, Madonna, Justin Bieber, Gustavo Dudamel, Coldplay’s PS22 Chorus, da kuma jaruman Sesame Street da The Muppets.

Advertisement

Ana sa ran shirin nishaɗin hutun rabin lokaci zai wuce mintuna 15 da aka saba warewa, domin bai wa mawaƙan damar gudanar da wasanninsu cikin kayatarwa.

Wasan ƙarshe na gasar, wanda za a fafata tsakanin Argentina da Sifaniya, ana sa ran zai jawo hankalin miliyoyin masu kallo a faɗin duniya, tare da nishaɗin da manyan taurarin waƙa za su gabatar kafin a ci gaba da wasan.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending