Sports
Italiya Ta Yi Watsi Da Tayin Trump Na Neman Ta Maye Gurbin Iran A Gasar Cin Kofin Duniya Ta 2026
Hukumar kwallon kafa ta kasar Italiya ta yi watsi da tayi da shugaban Amurka Donald Trump ya yi mata, na ganin ta maye gurbin Iran a gasar cin kofin duniya ta 2026, da za a gudanar a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Ministan harkokin wasanni na Italiya Andrea Abodi, ya ce wannan sam ba shawara ce da ta dace ba, yayin da shi ma ministan kudi na Italiya Giancarlo Giorgetti ya bayyana shawarar a matsayin abin kunya.
Dakarun Sojin Sun Dakile Harin ’Yan Ta’adda A Kukareta, Sun Kashe 24
Shi ko shugaban kwamitin Olympic na kasar, wanda ke da alhakin kula dukkan harkokin wasannin kasar Luciano Buonfiglio, cewa ya yi aikata hakan na zama wani babban laifi, domin cancanta ake bi sannan a samu damar zuwa gasar.
Jaridar The Financial Times ta rawaito cewa wani kusa a gwamnatin Amurka mai suna Paolo Zampolli, shi ne ya mika shawarar wannan zabi ga shugaba Trump da kuma shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Gianni Infantino.
Za a fara gasar a ranar 11 ga watan Yunin 2026, sannan a karkare a ranar 19 ga Yuli, to sai dai har yanzu Iran ba ta ce komai ba, game da shirin halartar gasar ko akasin haka, inda aka tsara buga wasanninta uku na rukuni a Amurka.
DW
