News
Gwamnatin Kano Ta Amince Da Kashe Naira Biliyan 55.48 Don Ayyukan Ci Gaban Al’umma
Majalisar Zartarwar Jihar Kano (EXCO) ta amince da aiwatar da ayyuka da shirye-shiryen raya jihar na Naira biliyan 55.48, inda fannin ilimi ya kasance wanda ya fi samun kaso mafi tsoka, yayin da aka kuma ware kuɗaɗe masu yawa domin ayyukan lafiya, hanyoyi, samar da ruwa, gidaje da ci gaban karkara.
An cimma wannan matsaya ne a taron Majalisar Zartarwa karo na 40 da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya jagoranta a Fadar Gwamnatin Kano.
Aƙalla Fasinjoji 68 Ne Suka Tsallake Rijiya Da Baya A Jirgin Enugu Air
Da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya ce majalisar ta amince da kashe jimillar Naira 55,475,406,487.82 domin aiwatar da muhimman ayyukan da za su inganta rayuwar al’ummar jihar.
Waiya ya ce gwamnatin ta ba fannin ilimi fifiko, inda ta amince da gyaran da sake fasalin makarantu, gina sabbin azuzuwa, samar da dakunan gwaje-gwaje, dakunan karatu, cibiyoyin fasahar sadarwa (ICT), kayan makaranta da kuma samar da lantarkin hasken rana a makarantu daban-daban.
Ya ce daga cikin manyan ayyukan da aka amince da su akwai gyaran Kwalejin Kimiyya ta Sani Bello da ke Dawakin Kudu kan Naira biliyan 1.02, gyaran Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Dawakin Tofa kan Naira miliyan 896.34, da kafa Cibiyar Koyon Zamani ta Maryam Abba Yusuf a Rijiyar Gwangwan kan Naira miliyan 312.29.
Hakazalika, majalisar ta amince da biyan bashin kuɗin ciyar da ɗaliban makarantun kwana da ya kai Naira miliyan 816.21, tare da gyaran motocin bas 31 na shirin ilimin yara mata da kuma samar da kayan koyarwa ga makarantu na musamman.
A bangaren lafiya kuwa, gwamnatin ta amince da gina da sake gyaran cibiyoyin kiwon lafiya a ƙananan hukumomi daban-daban, tare da samar da kayan aikin asibitoci da cibiyar kula da masu fama da cutar sikila ta jihar.
Haka kuma, an amince da ɗaga darajar cibiyoyin lafiya na Gano da Dukawa zuwa mataki na biyu, da faɗaɗa cibiyar lafiya ta Kofar Na’isa, tare da gyaran cibiyar lafiya ta Warawa.
A fannin gine-ginen hanyoyi, majalisar ta amince da gina hanyar Ungogo–Minjibir kan Naira biliyan 10.47, hanyar Kofar Waika–Turba–Gidan Siminti–Dorawar Dillalai kan Naira biliyan 3.67, da aikin hanyoyi da magudanan ruwa a Kasuwar Singer kan Naira biliyan 3.09.
Sauran ayyukan sun haɗa da sake gina hanyoyin Ali Yakasai da Tukur Road a Karamar Hukumar Nasarawa kan Naira biliyan 2.12, girka fitilun tituna masu amfani da hasken rana, ci gaba da faɗaɗa hanyoyi, gyaran gine-ginen gwamnati da kuma sabon ginin Majalisar Dokokin Jihar Kano.
Domin inganta samar da ruwa da tsaftar muhalli, gwamnatin ta amince da kashe sama da Naira biliyan 2.2 wajen samar da dizal ga cibiyoyin samar da ruwa, da Naira miliyan 558.1 domin biyan kuɗin lantarki ga Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Kano (KEDCO).
Haka kuma, an ware Naira miliyan 300 domin kwashe laka daga magudanan ruwa don rage barazanar ambaliya, yayin da aka amince da sama da Naira biliyan 4.1 domin ayyukan gina magudanan ruwa, shimfiɗa tayal da kawata muhalli.
A bangaren filaye da tsara birane, majalisar ta amince da biyan diyya da ta haura Naira biliyan 6.5 ga masu kadarorin da ayyukan hanyoyi suka shafa, musamman na Kano Northern Bypass da hanyar Gaya mai layi biyu.
Sannan ta amince da bayar da gudummawar Naira biliyan 1.169 ga shirin Rural Access and Agricultural Marketing Project (RAAMP), sayen kayan aikin zamani ga Gidan Rediyon Jihar Kano (KSBC), da kuma horas da jami’an yaɗa labarai na gwamnati.
Bugu da ƙari, majalisar ta amince da miƙa kudurorin dokoki guda biyar da suka shafi harkokin lafiya ga Majalisar Dokokin Jihar Kano, tare da amincewa da shigar jihar cikin shirin NG-CARES 2.0 domin faɗaɗa tallafin rayuwa ga al’ummomin da ke cikin buƙata.
Dangane da tsaro, Majalisar Zartarwar ta ayyana abin da aka fi sani da “Daba” a matsayin mummunar ɗabi’a da ba za a lamunta da ita ba, tare da umartar hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa su ƙara kaimi wajen daƙile wannan matsala.
Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya ce matakan da majalisar ta ɗauka sun nuna ƙudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da zuba jari a muhimman fannoni, domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’ummar Jihar Kano.
-
Opinion5 days ago
Ayyuka, Bin Diddigi, Biyan Kudi, Sakamako: Dabarun Kano Da Suka Zarce Jihohi 35
-
Opinion4 days ago
Tiriliyan ₦210 na Karya: Yadda Bala Wunti Ya Warware Dukkan Rudanin da Ya Mamaye Zaman Majalisar Dattawa Kan Asusun NNPC
-
News3 days ago
Likitan El-Rufai Ya Shiga Matsala Kan Zargin Bayar Da Rahoton Jinya Na Bogi
