Connect with us

News

Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Shekara 490 Kan Tsohon Shugaban Bankin NEXIM

Published

on

1788977638149

Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 490 da aka yanke wa tsohon Manajan Daraktan Bankin NEXIM, Robert Orya, kan zargin almundahanar Naira biliyan 2.4.

Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Talata, inda ta yi watsi da karar da Orya ya shigar yana kalubalantar hukuncin Babbar Kotun Abuja.

An Buɗe Yaƙin Neman Zaɓen Gwamna Da Majalisun Jihohi A Najeriya

Kotun ta ce karar ba ta da hujjar da za ta sa a sauya hukuncin.

A watan Fabrairun 2026, Babbar Kotun Abuja ta yanke wa Orya hukuncin shekaru 10 a kan kowanne daga cikin tuhume-tuhume 49 da aka same shi da su.

Sai dai kotun ta bayar da umarnin gudanar da hukuncin a lokaci guda, ma’ana a zahiri zai yi zaman gidan yari na shekaru 10.

Advertisement

Hukumar EFCC ta tuhumi Orya da amfani da mukaminsa wajen samun bashi daga NEXIM Bank, ciki har da zargin kafa wani kamfani da ya yi amfani da sunayen mutanen da ba su wanzu ko kuma ba su amince ba wajen samun bashi da ba a biya ba.

Orya ya kasance Manajan Daraktan NEXIM Bank daga shekarar 2009 zuwa 2016, kafin a gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume 49 a shekarar 2021.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending