Connect with us

Business

Dangote Na Duba Yiwuwar Gina Sabuwar Matatar Mai A Kenya Mai Tace Ganga 650,000 A Kullum

Published

on

08620dc5bd71b01c3c159758ac65e760d3ba5d8c55e2e1c360f1181f5896edaf (1)

Attajirin Nijeriya Aliko Dangote na tunanin Kenya a matsayin wurin da zai gina sabuwar matatar mansa a Gabashin Afirka mai iya tace ganga 650,000 a rana, in ji rahoton Financial Times a ranar Lahadi, inda jaridar ta ruwaito labarin dangane da hirar da aka yi da shi.

“Ina so na karkata zuwa Mombasa saboda Mombasa na da tashar jiragen ruwa mai fadi da zurfi,” in ji Dangote a cikin hirar.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Cafke Mutane Uku Masu Buƙata Ta Musamman Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi

Rahoton ya zo ne bayan Shugaban Kenya William Ruto ya ce a watan da ya wuce ƙasashen Gabashin Afirka na tattaunawa kan shirin gina matatar mai ta haɗin gwiwa a tashar jiragen ruwa ta Tanga a Tanzania wadda aka tsara bisa misalin ta Dangote na Nijeriya.

Advertisement

Sai dai, Dangote a cikin hirar ya kwatanta Mombasa ta Kenya da tashar Tanga ta Tanzania, ya ce, “Mutanen Kenya sun fi amfani da mai. Tana da tattalin arziki mafi girma.”

Zai iya kashe har zuwa dala biliyan 17

Advertisement

“Komai na hannun Shugaba Ruto,” in ji shi.

“Abin da Shugaba Ruto ya ce shi zan yi,” kamar yadda ya ƙara da cewa.

Advertisement

Dangote ya kiyasta cewa gina wannan matatar zai kai dala biliyan 15 zuwa 17, in ji rahoton FT.

A halin yanzu Gabashin Afirka na shigo da dukkan samfuran mai da aka tace, mafi yawansu daga Gabas ta Tsakiya, wanda ke sa yankin fuskantar matsaloli idan aka samu tangardar samar da mai da tashin farashi kamar yadda aka gani yayin yakin Amurka da Isra’ila kan Iran.

Advertisement

Mafi arzikin Afirka, Aliko Dangote, a wani taron tattaunawar ababen more rayuwa a Nairobi a watan da ya wuce, ya ce zai iya yin sak matatar mansa ta Nijeriya a Gabashin Afirka, muddin gwamnatocin yankin sun goyi bayan wannan yunƙuri.

Matatar Dangote mai darajar dala biliyan 20 a cibiyar kasuwanci ta Nijeriya da ke Legas ta fara aiki a 2024.

Advertisement

 

 

Advertisement

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending