Connect with us

News

An Cafke Mutane Biyar Kan Safarar Miyagun Ƙwayoyi Zuwa Gidan Yari Ta Jiragen Sama Marasa Matuka

Published

on

IMG 20260811 234510 716

Rundunar ’yan sandan Faransa ta kama wasu mutane da ake zargi da hannu wajen safarar miyagun ƙwayoyi da wasu haramtattun kayayyaki zuwa cikin gidan yari ta amfani da jirage marasa matuƙa, wato drones.

Binciken hukumomin tsaron Faransa ya nuna cewa wata ƙungiya ta ƙware wajen amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai kayayyaki zuwa gidan yarin Villeneuve-lès-Maguelone, a kudancin ƙasar.

Rundunar Sojin Ƙasa Ta Buɗe Shafin Daukar Sabbin Ma’aikata Na Short Service

Rahotanni sun ce ƙungiyar tana karɓar kuɗi domin kai kayayyaki daban-daban zuwa cikin gidan yarin, ciki har da miyagun ƙwayoyi, wayoyin hannu, sigari da barasa.

Hukumomin sun ce ana gudanar da wannan aika-aika ne ta hanyar wata ƙungiya da ake zargin wasu fursunoni da ke cikin gidan yarin ne ke jagoranta, tare da haɗin gwiwar mutanen da ke wajen gidan yarin.

A wani samame da aka gudanar a yankin Montpellier a ranar 22 ga Yuni 2026, jami’an tsaro sun kama mutane bakwai, ciki har da wasu biyu da ake zargi da kasancewa jagororin hanyar sadarwar, waɗanda tuni suke tsare a gidan yarin.

Advertisement

An kuma kwato wayoyin hannu da dama, kwamfuta, na’urar sarrafa jirgin mara matuƙi da kuma tsabar kuɗi har €20,500 da ake zargin an samu daga ayyukan isar da kayayyakin.

Binciken ya kuma gano cewa ana cajin kusan €150 kan kowace isarwa ta jirgin mara matuƙi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending