Connect with us

News

Karya Darajar Naira Da Tinubu Ya Yi Ya Kara Jefa ‘Yan Najeriya Cikin Talauci —Olusegun Obasanjo

Published

on

obasanjo 2
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aiwatar, musamman rage darajar naira, sun ƙara jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin talauci.

Obasanjo ya bayyana hakan ne a yayin taron koli kan tattalin arzikin Afirka na shekarar 2026 da jaridar Financial Times ta shirya a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, ranar Laraba.

 

Tsohon shugaban ƙasar ya ce faɗuwar darajar naira cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ta rage ƙarfin sayen ’yan Najeriya, lamarin da ya taimaka wajen ƙara ta’azzara matsalar talauci a ƙasar.

 

A cewarsa, darajar naira ta faɗi daga kusan naira 500 zuwa dala ɗaya zuwa naira 1,500, matakin da ya ce ya yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin jama’a.

Advertisement

 

“Ba mu rayuwa a keɓe a matsayin ƙasa ba. Muna hulɗa da sauran ƙasashen duniya. Amma cikin dare ɗaya, ka rage darajar kuɗinka da kashi 300 cikin 100, naira ta tashi daga naira 500 zuwa dala ɗaya zuwa naira 1,500,” in ji shi.

 

Obasanjo ya ƙara da cewa irin wannan mataki ya jefa ’yan Najeriya cikin talauci, yana mai cewa ba za a iya cewa hakan alheri ne ga ƙasar ba.

 

Ya ce sakamakon sauye-sauyen ya bayyana ne ta hanyar raguwar ƙarfin sayen jama’a da kuma ƙarin wahalhalun tattalin arziki da suke fuskanta.

Advertisement

 

A watan Mayun 2023 ne Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, matakin da ya jawo tashin farashin fetur da kuɗin sufuri a faɗin ƙasar.

 

Haka kuma, a watan Yunin 2023, gwamnatin ta fara sauye-sauye a kasuwar canjin kuɗaɗen ƙasashen waje, inda aka bai wa naira damar samun darajarta bisa yanayin kasuwa, tare da kawo ƙarshen tsarin farashin canji daban-daban.

 

Gwamnatin Tinubu ta bayyana cewa an aiwatar da sauye-sauyen ne domin inganta kasuwar canjin kuɗi, jawo masu zuba jari daga ƙasashen waje da kuma magance matsalolin da suka dabaibaye harkokin kuɗi.

Advertisement

Sai dai matakan sun zo ne a daidai lokacin da naira ke fuskantar faɗuwar daraja, hauhawar farashin kayayyaki da tsadar kayan da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Wannan ya ƙara tsananta matsin tattalin arziki ga iyalai da ’yan kasuwa, musamman sakamakon tashin farashin kayan abinci, sufuri da sauran muhimman kayayyakin masarufi.

 

 

DAILY TRUST 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending