News
NAAT Ta Ce Har Yanzu Akwai Bashin Haƙƙoƙin Ma’aikata Da Gwamnatin Kano Bata Biya Ba A Jami’ar Wudil
Ƙungiyar Ma’aikatan Fasaha ta Jami’a ta Ƙasa (NAAT), reshen Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil a Jihar Kano, ta ce har yanzu akwai haƙƙoƙin mambobinta da ba a biya ba, duk da ikirarin cewa an kammala biyan basussukan ma’aikatan jami’ar.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar bayan taron mambobinta a ranar 20 ga Oktoba, 2026.
NAAT ta ce wasu daga cikin basussukan da har yanzu ba a biya ba sun haɗa da alawus ɗin haɗarin aiki na kashi 50 cikin 100, kuɗaɗen ƙarin tallafin ɗaliban fasaha, da kuma jinkirin aiwatar da yarjejeniyar NAAT da Gwamnatin Tarayya ta shekarar 2026 kan tsarin albashin mambobinta.
A cewar sanarwar, taron ƙungiyar ya umarci shugabanninta da su sanar da Gwamnatin Jihar Kano da mahukuntan jami’ar game da waɗannan matsaloli, domin a ɗauki matakin magance su.
Ƙungiyar ta kuma yi gargaɗin cewa za ta iya shiga yajin aiki idan ba a biya haƙƙoƙin mambobinta ba.
Shugaban NAAT na jami’ar, Comrade Bamalili Mukhtar Umar, ne ya sanya wa sanarwar hannu.
An aika da kwafin sanarwar ga Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Kwamishinan Ilimi da Ayyuka na Musamman, da Mataimakin Shugaban Jami’ar, da sauran hukumomin da abin ya shafa.
-
News6 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News5 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News6 days ago
Musa Illiyasu Kwankwaso Ya Taya Sanata Lado Murnar Cika Shekaru 60, Ya Kira Shi Gogaggen Ɗan Siyasa

