Connect with us

News

“Ba’a Lashe Zabe Da Fariya” Jam’iyyar ADC Ta Mayarwa Da Wike Martani

Published

on

Rivers Gov Nyesom Wike

Jam’iyyar ADC reshen Jihar Ribas ta ce babu wani ɗan siyasa da zai iya lashe zaɓen 2027 ta hanyar fariya, barazana ko yi wa jama’a alkawuran da ba za a cika ba.

Shugaban ADC na jihar, Chukwudi Dimkpa, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a Fatakwal ranar Litinin, yana mayar da martani ga kalaman Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Mun Ba Wa Ministan Tsaro kwana 7 Ya Janye Kalamansa Kan Mahaifinmu Ko Mu Kai Kararsa Kotu  —Iyalan El-Rufai

Wike ya yi ikirarin cewa ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na ADC, Rotimi Amaechi, zai sha kaye da misalin ƙarfe 12 na rana a ranar zaɓe.

Sai dai Dimkpa ya ce sakamakon zaɓe ba Wike ne zai bayyana shi ba, domin al’ummar Rivers ne za su kada ƙuri’a, sannan INEC ce za ta bayyana wanda ya yi nasara.

Ya kuma zargi Wike da amfani da lokacin jana’izar mahaifiyar Amaechi wajen gudanar da taron siyasa da kuma yi masa ba’a, yana mai cewa hakan ya kasance rashin tausayi da abin kunya.

Advertisement

Dimkpa ya bukaci al’ummar Rivers da kada su ji tsoron kowane ɗan siyasa, su kuma zaɓi shugaba nagari da zai inganta rayuwarsu a zaɓen 2027.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending