Business
Farashin Kaya Ƙaru Zuwa Kashi 15.38 A Najeriya
Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) ta sanar cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ya ƙaru zuwa kashi 15.38 cikin ɗari a watan Maris na shekarar 2026, daga kashi 15.06 da aka samu a watan Fabrairu.
A cikin rahoton Consumer Price Index (CPI) da hukumar ta fitar, an bayyana cewa wannan ƙarin na maki 0.32 shi ne karo na biyu a jere da ake samun tashin farashi a bana, kuma shi ne karo na farko cikin kusan shekara guda da aka samu irin wannan.
Zan Hakura Da Tsayawa Takara Daga Zaben 2027 —Atiku
Hukumar ta danganta wannan hauhawar da tsadar kayan abinci, inda farashin kayayyakin yau da kullum kamar doya, tumatir da rogo ya ƙaru sosai. Haka kuma, an lura da tashin farashin sauran muhimman kayayyaki da suka haɗa da burodi, hatsi da kayan lambu.
Masana tattalin arziki na ganin cewa hauhawar farashin na da alaƙa da tsadar makamashi kayayyaki da har yanzu ke addabar tattalin arziki .
