Connect with us

News

Wasu Kansiloli Na Zargin Ciyaman Da Daukar ‘Yan Daba Domin Kai Musu Hari A Kano

Published

on

Fadan Daba Ya Haifar Da Zaman Dardar A Unguwanne Da Dama A Cikin Kano

Wasu kansiloli biyu na Ƙaramar Hukumar Fagge da ke Jihar Kano sun zargi Shugaban Ƙaramar Hukumar, Alhaji Salisu Usman Masu, da hannu wajen shirya harin da wasu da ake zargin ’yan daba ne suka kai musu bayan wani taro da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya halarta.

Kansilan ’Yanmata Gabas, Shamsu Ali Umar, da Kansilan Fagge D1, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar, Sani Muhammad, sun ce lamarin ya faru ne a harabar Asibitin Cutar Masu Yaɗuwa (IDH) bayan kammala taron da gwamnan ya halarta a ranar Litinin.

Majalisar Dokokin Kano Ta Dakatar Da Shugabannin Kananan Hukumomin Bagwai, Rogo Da Bebeji 

Aminiya ta ruwaito Cewa Sani Muhammad ya bayyana cewa, yayin da suke shirin komawa motocinsu, wasu mutane kimanin 30 ɗauke da makamai suka afka musu tare da yi musu duka.

Ya ce an buge shi da sanda a kai har ya samu rauni, yayin da wani kansilan ma ya ji rauni. A cewarsa, jami’an tsaro ne suka shiga tsakani suka ceto shi, yayin da sauran kansilolin suka tsere domin kauce wa harin.

Advertisement

Kansilolin sun yi zargin cewa harin ya samo asali ne daga saɓanin siyasa da ke tsakaninsu da shugaban ƙaramar hukumar, inda suka ce an shirya shi tun kafin ranar taron.

Sun kuma ce za su bi hanyoyin doka domin neman a binciki lamarin tare da hukunta waɗanda suka aikata harin. Haka kuma sun bayyana cewa suna nazarin ɗaukar matakin tsige shugaban ƙaramar hukumar.

Sai dai, Jaridar Inda Ranka ta fahimci cewa ƙoƙarin jin ta bakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Fagge, Alhaji Salisu Usman Masu, kan zarge-zargen bai yi nasara ba, domin bai amsa kiran waya ko saƙonnin da aka aika masa ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending