Connect with us

News

NEJA: Mutane 33 Sun Mutu A Hannun jami’an NSCDC

Published

on

FB IMG 1789684273329

Akalla mutane 33 da ake zargi da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba sun mutu yayin da suke tsare a hannun jami’an Hukumar NSCDC a Jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Alhamis, 17 ga Satumba, 2026, bayan hukumar ta kama mutanen a yayin samamen da ta gudanar a yankin M.I. Wushishi da ƙauyen Lukoto a ranakun 15 da 16 ga Satumba.

Bauchi: Ɗalibin Sakandare Ya Baje Kolin Motar Gas, Jirgin Sama Da Sauran Ƙirƙire-Ƙirkirensa

Kwamandan NSCDC na Jihar Neja, Suberu Siyaka Aniviye, ya bayyana cewa an gano cewa mutane da dama daga cikin waɗanda aka kama sun mutu yayin da suke tsare a hannun hukumar.

A cewar hukumar, ana zargin cewa wata cuta ce ta haddasa mutuwar mutanen, sai dai ba a bayyana sunan cutar ba ko kuma tabbatar da cewa ita ce musabbabin mutuwar ba.

An kai gawarwakin zuwa Babban Asibitin Minna domin gudanar da bincike da gwaje-gwajen lafiya da za su taimaka wajen gano ainihin musabbabin mutuwarsu.

Advertisement

A gefe guda kuma, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Neja, Adamu Elleman, ya bayar da umarnin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.

Kwamishinan ya umarci Sashen Binciken Manyan Laifuka (SCID) na rundunar ’yan sanda da ke Minna da su  jagoranci binciken domin gano abubuwan da suka haifar da mutuwar mutanen.

 

 

SOLACEBASE

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending