Connect with us

Entertainment

“Idan Aka Yi Maguɗi A Zaɓen Gwamnan Jihar Osun, Zan Kai Ƙorafi Wajen Trump” – Davido

Published

on

images (3)

Fitaccen mawaƙin Najeriya, David Adeleke (Davido), ya yi gargaɗin cewa zai kai ƙorafi ga Shugaban Amurka, Donald Trump, idan aka samu maguɗi ko wata rashin gaskiya a zaɓen gwamnan jihar Osun mai zuwa.

Advertisements
Advertisements

Davido ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa kai tsaye a shafukan sada zumunta, inda ya ce ba zai amince da duk wani yunƙuri na karkatar da sakamakon zaɓe ba.

Advertisements

Gwamna Yusuf ya jagoranci daurin auren gata na zawarawa da ’yan mata 1,500 a Kano

Advertisements
Advertisements

Ya kuma yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin lumana, gaskiya da adalci domin kare martabar dimokuraɗiyyar Najeriya.

Kalaman na Davido sun jawo ce-ce-ku-ce a kafafen sada zumunta, inda mutane ke ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu kan batun yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnan jihar Osun.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending