Interview
Tuzurai 29 Sun Kashe Kansu Saboda Rashin Samun Aure A Indiya
Akalla Tuzurai 29 ne suka mutu sakamakon kashe kansu a gundumar Jalgaon da ke jihar Maharashtra a Indiya, bayan sun kasa samun abokan aure, a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.
Bayanan rundunar ‘yan sandan yankin sun nuna cewa mutane 443 ne suka mutu sakamakon kashe kansu tsakanin 1 ga Janairu zuwa 30 ga Yuni 2026. Daga cikinsu akwai maza 383, mata 29, yara maza takwas da ‘yan mata 11.
Yanbindiga Sun Harbe Babba Ma’aikacin Jami’ar NOUN A Zamfara
Sufeto-Janar na ‘yan sandan Jalgaon, Shrikant Dhivare, ya ce rashin samun abokiyar aure na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen jefa wasu daga cikin matasan cikin matsananciyar damuwa.
Ya ce sauyin abubuwan da ake nema wajen zabar abokin aure, musamman yadda wasu mata ke fifita rayuwar birane, ya sa wasu maza da ke zaune a karkara samun aure ya zama musu wahala.
Bayanan sun kuma nuna cewa matsalar shaye-shayen barasa ce ta haddasa mutuwar mutane 90, yayin da aka danganta mutane 87 da damuwa da matsalar tabin hankali. Haka kuma, rikicin iyali ya haddasa mutuwar mutane 78, yayin da basussuka suka jawo wasu mutane 52 kashe kansu.
‘Yan sanda sun ce matsalar tana bukatar kulawa daga al’umma, musamman ganin yadda ake samun sauyin zamantakewa da tattalin arziki da kuma rashin daidaiton yawan maza da mata a shekarun aure.
