News
Dan Najeriya Ya Mutu Sanadiyyar Aikin Kara Girman Mazakutarsa
Wani ɗan kasuwa ɗan asalin Najeriya da Birtaniya, Igho Ubiribo mai shekaru 43, ya mutu bayan ya yi wata tiyata ta ƙara girman azzakarinsa a birnin Bangkok na ƙasar Thailand.
Rahoton ya ce an yi masa allurar wani sinadari mai suna hyaluronic acid a mazakutarsa. Bayan aikin, ya fara jin ciwon ƙirji tare da suma sau biyu a daidai lokacin da matarsa ke masa tausa.
Gidauniyar Yahaya Sarki Ta Tallafa Wa Mata Da Matasa 200 A Birnin Kebbi
An garzaya da shi asibiti, inda likitoci suka gano cewa wani gudan jini ne ya toshe wata jijiya da ke kai jini zuwa huhu.
Daga bisani ya mutu a ranar 6 ga Maris, bayan likitoci sun kwashe sama da mintuna 100 suna ƙoƙarin ceto rayuwarsa.
Binciken bayan mutuwarsa ya nuna cewa sinadarin da aka yi amfani da shi wajen ƙara girman al’aurar ne ya shiga huhunsa, lamarin da ya haddasa matsalar.
-
News6 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News3 days ago
Matasa A Unguwar Gama Sun Yi Kira Ga Majalisar Dokokin Kano Ta Ladabtar Da Ɗan Majalisar Nassarawa Kan Zargin Cin Zarafin Gwamna
-
News4 days ago
Shugaba Tinubu Ya Ce Ba Zai Dawo Da Tallafin Man Fetur Ba Kuma Ba Ya Da-na-sanin Cire Shi

