Connect with us

Uncategorized

Kotu Ta Ba Da Belin Ƴar Jarida Farida Isiak Bayan Tsare Ta A Kaduna

Published

on

IMG 20261022 WA0112 750x645
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Wata kotu da ke zamanta a Kawo, cikin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna, ta bayar da belin ƴar jarida mai shekaru 23, Farida Isiak, wadda jami’an ƴan sanda suka tsare tare da iyayenta bisa wani saɓani da ya shafi sayen gawayi.

Alƙalin kotun, Alhaji Tureta, ya bayar da belin Farida har zuwa ranar 3 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Shugaba ‎Tinubu Ya Nada Tsohon Shugaban DSS, Yusuf Bichi, Sabon Muƙami

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne daga saɓani tsakanin mahaifiyar Farida da wata maƙwabciyarsu kan sayen gawayi a Mararaban Jos, da ke Jihar Kaduna.

 

Farida, wadda ke aiki da gidan rediyon Nagarta da ke Kaduna, an ruwaito cewa an kai ta ofishin ƴan sanda da misalin ƙarfe 10 na dare ranar 20 ga Oktoba, bayan an riga an tsare iyayenta.

Advertisement

Wani ɗan gidan nasu ya bayyana cewa Farida ta samu labarin kama mahaifiyarta ne a lokacin da take wurin aiki, inda daga bisani ta wallafa saƙo a shafinta na Facebook tana sukar ƴan sanda kan lamarin.

Da yake magana kan batun, shugaban gidan rediyon Nagarta, Alhaji Nasiru Yakubu Birnin Yero, ya shaida wa wakilinmu cewa gidan rediyon ba shi da hannu a rikicin da ya faru tsakanin iyalan Farida da maƙwabtansu.

Sai dai ya bayyana cewa an daɗe ana samun rashin jituwar fahimta tsakanin wasu jami’an ƴan sanda da ma’aikatan gidan rediyon, sakamakon yadda kafar watsa labaran ta bayar da rahoton kisan wata malama a Mararaban Jos.

Birnin Yero ya shawarci ƴan jarida da su yi taka-tsantsan wajen wallafa saƙonni a shafukan sada zumunta, musamman waɗanda ka iya haifar da sabani ko jawo musu matsaloli.

An bayar da belin Farida ne domin ta ci gaba da bin matakan shari’a, yayin da ake sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron ƙarar a ranar 3 ga Nuwamba, 2026.

 

Advertisement

 

 

Leadership

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending