Sports
Shugaban Hukumar Wasanni Ta Kano Ya Jagoranci Rufe Gasar Kwallon Tebur Ta Ranar Yancin Kai 2026
Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, ya jagoranci bikin rufe gasar Kano State Table Tennis Independence Day Tournament 2026, wadda Kungiyar Wasan Kwallon Tebur ta Jihar Kano ta shirya domin murnar cikar Najeriya shekaru 66 da samun ‘yancin kai.
An gudanar da gasar ne a Cibiyar Wasanni dake Kwalejin Sa’adatu Rimi, inda sama da ‘yan wasa 36 suka fafata a matakai daban-daban tare da nuna kwarewa da bajinta.
A sakamakon gasar, MBA MBA Uzorma Dimkpa ya zama zakara ya samu kyautar naira 100,000 sai kuma dan wasa Saminu Adam ya zo na biyu ya samu kyautar naira 50,000, yayin da Abdulbaki Yunusa da Raka One suka kammala a mataki na uku, inda kowannensu ya samu naira 25,000.
Da yake rufe gasar, Alhaji Muhammad Tukur Babangida ya yaba wa Kungiyar Wasan Kwallon Tebur ta Jihar Kano da kwamitin shirya gasar bisa kokarin da suka yi wajen gudanar da gasar cikin nasara, tare da jaddada muhimmancin tallafa wa matasa da bunkasa wasanni a jihar.
Shi kuwa wanda ya dauki nauyin shirya gasar, Malam Bashir Umar, ya bayyana cewa an shirya gasar ne domin tallafa wa matasan ‘yan wasa da kuma bayar da gudunmawa wajen ci gaban wasanni, inda ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da tallafa wa harkokin wasanni.
A nasa bangaren, Mataimakin Shugaban Kungiyar Wasan Kwallon Tebur ta Jihar Kano, Malam Yasa’a Wada Abubakar, ya bayyana cewa gasar ta kasance wata hanya ta hada kan masu sha’awar wasan kwallon tebur tare da murnar ranar ‘yancin kan Najeriya.
A yayin bikin rufe gasar, kungiyar ta karrama Shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Alhaji Muhammad Tukur Babangida, da lambar girmamawa bisa goyon baya da gudunmawar da yake bayarwa wajen bunkasa wasanni a jihar.
Sa Hannu:
Ashiru Rabiu Gidan Tudu,
Jami’in Yaɗa Labarai,
Hukumar Wasanni ta Jihar Kano
1st October, 2026.
