News
Hare-haren Ta’addanci Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 835 A Najeriya Cikin Wata Guda – Rahoto

Wani sabon rahoton tsaro ya bayyana cewa aƙalla mutane 835 ne suka mutu sakamakon hare-haren ƴan bindiga, ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da sauran matsalolin tsaro a faɗin Najeriya cikin watan Oktoban 2026.
Rahoton, wanda kamfanin nazarin bayanan tsaro na SARI Global ya fitar, ya ce an samu aukuwar hare-hare da sauran matsalolin tsaro guda 612 a jihohi 36 na ƙasar da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja a cikin watan.
Gwamnatin Nijar ta haramta fitar da gyaɗa zuwa ƙasashen waje
Rahoton ya nuna cewa ƴan bindiga da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya ne suka fi kai hare-hare tare da haddasa asarar rayuka a karon farko cikin watannin baya-bayan nan.
Daga cikin munanan hare-haren da rahoton ya ambata akwai kisan kiyashin da aka yi a wata kasuwa a Jihar Taraba, da kuma toshe hanyoyi da ƴan bindiga suka riƙa yi a Jihar Zamfara.
Haka kuma, kisan malamin addinin Musulunci, Malam Yahaya Ibrahim Masussuka, na daga cikin abubuwan da suka ƙara dagula al’amuran tsaro a ƙasar.
Rahoton mai taken SARI Global’s Nigeria Monthly Security Overview for October 2026 ya nuna cewa an samu ƙaruwar hare-hare da asarar rayuka idan aka kwatanta da watan Satumba.
A cewar rahoton, hare-haren sun ƙaru da kashi 14 cikin 100, yayin da adadin mutanen da aka kashe ya ƙaru da kashi 42 cikin 100 a watan Oktoba idan aka kwatanta da watan Satumba.
Kamfanin ya bayyana wannan a matsayin mafi girman ƙaruwar mace-mace da aka samu cikin wata guda a watannin baya-bayan nan.
Rahoton ya kuma nuna cewa a watan Yunin 2026 an samu hare-hare 882 da suka yi sanadin mutuwar mutane 792, yayin da a watan Yuli aka samu hare-hare 596 da suka kashe mutane 570.
SARI Global ya ƙware wajen tattara bayanan tsaro, nazarin rikice-rikice da kuma samar da bayanan da ke taimaka wa ƙungiyoyi wajen gudanar da ayyukansu a yankunan da ke fama da matsalolin tsaro.
