News
Jihar Kano Za Ta Karɓi Bakuncin Babban Taron Bunkasa Kiwon Kaji Na Arewacin Nijeriya

Jihar Kano za ta karɓi bakuncin babban taron masana’antar kiwon kaji na Arewacin Nijeriya (Northern Nigeria Poultry Conference and Exhibition 2026), wanda ake sa ran zai haɗa manoman kaji, ’yan kasuwa, masu zuba jari da masana harkar noma.
Shugaban Ƙungiyar Manoman Kaji ta Nijeriya (PAN), reshen Jihar Kano, Dr Usman Gwarzo, ne ya bayyana hakan, inda ya ce za a gudanar da taron na tsawon kwanaki biyu, daga ranar 18 zuwa 19 ga watan Nuwamba, 2026.
Jami’an Ƴansanda Sun Kubutar Da Mutane 19 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Zamfara.
Za a gudanar da taron ne a cibiyar taro ta Afficient Event Centre da ke lamba 7A, Sultan Nasarawa GRA, a cikin birnin Kano.
Taken taron shi ne: “Mayar da ƙalubalen kiwon kaji zuwa ci gaba mai ɗorewa ta hanyar ƙirƙire-ƙirƙire, kasuwanci da zuba jari.”
Taron na da manufar tattauna matsalolin da ke fuskantar masana’antar kiwon kaji tare da lalubo hanyoyin bunƙasa harkar ta hanyar amfani da fasaha, ƙarfafa kasuwanci da jawo hankalin masu zuba jari.
Haka kuma, taron zai ba manoman kaji, masu sarrafa kayan amfanin kaji, masu bincike da masu tsara manufofi damar musayar ra’ayoyi da ƙulla dangantakar kasuwanci domin inganta harkar kiwon kaji a Arewacin Nijeriya da Afirka ta Yamma.
Masu shirya taron na sa ran samun mahalarta sama da 2,000, masu baje kolin kayayyaki da masu ɗaukar nauyi sama da 100, da kuma sama da masana da masu gabatar da jawabai 50 daga cikin gida da ƙasashen waje.
Haka kuma, za a gudanar da zaman tattaunawa da na ƙwarewa sama da 20, inda za a tattauna batutuwan da suka shafi samar da kaji, kula da gonakin kiwo, jin daɗin dabbobi, ƙara yawan amfanin gona da kuma samun riba mai ɗorewa.
Ana sa ran taron zai buɗe sabbin damarmakin zuba jari, samar da haɗin gwiwar kasuwanci, inganta hanyoyin samun kasuwa da kuma ƙarfafa alaƙa tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar.
Masu shirya taron na fatan hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkar kiwon kaji, samar da ayyukan yi, rage matsalar ƙarancin abinci da kuma bunƙasa tattalin arzikin Arewacin Nijeriya.
