News
Sama Da Mutum 50 Ne Suka Mutu Sakamakon Arangamar ’Yan Bindiga Da ’Yan Sa-kai A Zamfara

Akalla mutum 53 ne suka mutu sakamakon arangamar da ta barke tsakanin ’yan bindiga da ’yan sa-kai a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Zoma da ke Ƙaramar Hukumar Bukkuyum, bayan ’yan bindigar sun yi garkuwa da wasu mutane a Ƙaramar Hukumar Gummi da ke makwabtaka da yankin.
Wani mai riƙe da sarautar gargajiya a yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa ’yan sa-kai sun samu labarin cewa ’yan bindigar na kan hanyarsu ta zuwa yankin, lamarin da ya sa suka yi musu kwanton ɓauna.
Ya ce a yayin musayar wutar, ’yan sa-kai sun kashe ’yan bindiga 44, yayin da tara daga cikinsu suka rasa rayukansu.
Ya ƙara da cewa an kashe wani fitaccen kwamandan ’yan bindiga mai suna Jijji, wanda ake zargi da jagorantar sace mutanen da suka haddasa arangamar.
Wasu mazauna ƙauyen Zoma da AFP ta zanta da su sun tabbatar da faruwar lamarin da kuma adadin waɗanda suka mutu.
A halin yanzu, rundunar sojojin Nijeriya na ci gaba da gudanar da ayyukan musamman na yaƙi da ’yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin ƙasar.
Matsalar tsaro da tsadar rayuwa na daga cikin manyan ƙalubalen da ke jan hankalin al’ummar Nijeriya a daidai lokacin da ƙasar ke tunkarar zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
