News
Gobara Ta Tashi A Wata Kasuwa A Legas

Hukumar kashe gobara ta Jihar Legas ta yi nasarar shawo kan wata gobara da ta tashi a kasuwar Ola da ke yankin Adedeji, Itire, a ƙaramar hukumar Surulere ta jihar.
Babbar jami’ar hukumar, Margaret Abimbola Adeseye, ta bayyana cewa sun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 10:12 na safiyar ranar Asabar.
Gwamnatin Bauchi Ta Dakatar Da Sarkin Lame Kan Zargin Karbar Haraji Ba Bisa Ka’ida Ba
Ta ce hukumar ta tura jami’an kashe gobara daga ofisoshinta na Sari Iganmu da Isolo zuwa wurin domin shawo kan lamarin.
A cewarta, gobarar ta shafi wani gini mai hawa ɗaya, amma jami’an sun yi nasarar kashe ta tare da hana ta yaɗuwa zuwa sauran sassan ginin.
Hukumar ta ƙara da cewa za ta fitar da ƙarin bayani kan musabbabin gobarar da sauran abubuwan da suka faru bayan kammala bincike.
