News
Ronaldo Ya Ce Bai Yi Murabus Daga Buga Wa Portugal Wasa Ba
Kyaftin Portugal Cristiano Ronaldo ya bayyana cewa ba yi ritaya daga buga wa ƙasarsa ƙwallon ƙafa ba, amma ya cancanci a hukunta shi saboda barin tawagar Portugal sakamakon “saɓa alƙawarin da kocin tawagar ya yi masa”.
Kyaftin din, mai shekaru 41, ya bar sansanin tawagar ƙasarsa a gasar Nations League bayan da aka ajiye shi a benci ba tare da an saka shi wasa ba a karawar da suka yi da Norway, sannan ya gano cewa ba za a saka shi a jerin ‘yanwasan farko ba a wasan da za su yi da Denmark.
Gwamnatin Legas Ta Kama Mabarata 62 A Kan Tituna
Ronaldo ya kuma nemi afuwar abokan wasansa na tawagar ƙasarsa, da ‘yankallo da ‘yankasar ta Portugal saboda matakin da ya ɗauka wanda ya ce bai kamata ba.
A cikin wata doguwar sanarwa, tsohon ɗanwasan na Real Madrid da Manchester United ya ce ya kamata a hukunta shi saboda abin da ya aikata, saboda abin da ya yi bai kamata ba, duba da kasancewarsa kocin tawagar ta Portugal.
