Connect with us

Labarai

Ba A Buƙatar Rahoton Jami’an Ƴansanda Kafin Duba Wanda Aka Harba —Sufeto-Janar

Published

on

images (10)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Sufeto Janar na Rundunar ’Yan sandan Nijeriya, Olatunji Disu, ya buƙaci asibitoci da ma’aikatan lafiya a faɗin ƙasar da su riƙa ba wa waɗanda suka samu raunukan harbin bindiga agajin gaggawa ba tare da jiran rahoton ’yan sanda ba.

Disu ya ce bai kamata a hana ko a jinkirta yi wa waɗanda suka jikkata magani saboda rashin rahoton ’yan sanda ba, yana mai jaddada cewa ceton rayuka ya kamata ya zama babban abin da ma’aikatan lafiya suka fi ba da muhimmanci.

Ƙungiyar Arewa Women Health ta gudanar da taron Makon ’Ya Mace a Kano

Ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin rundunar ’yan sandan a X ranar Alhamis, inda ya tabbatar da cewa ba za a hukunta ma’aikatan lafiya ko mutanen da suka taimaka wa waɗanda suka jikkata a lokacin da suke buƙatar agajin gaggawa ba.

Sufeto Janar ɗin ya bayyana cewa samun rahoton ’yan sanda ba sharaɗi ba ne kafin fara yi wa duk wanda ya samu raunin harbin bindiga magani, yana mai cewa bai kamata a jinkirta kulawar lafiya saboda wasu buƙatu na gudanarwa ba.

Ya buƙaci likitoci, ma’aikatan jinya, ungozomomi da sauran ma’aikatan kiwon lafiya da su riƙa tabbatar da cewa sun ba wa masu raunukan harbin bindiga agajin gaggawa da zarar sun isa asibiti.

Advertisement

Haka kuma, Disu ya yi kira ga al’umma da su riƙa taimaka wa waɗanda suka jikkata ko suka samu kansu cikin yanayin da ke buƙatar agajin gaggawa, ba tare da tsoron fuskantar hukunci saboda taimakon da suka bayar ba.

Ya jaddada cewa taimaka wa mutum a lokacin da yake cikin haɗarin rasa rayuwarsa abu ne mai muhimmanci, kuma ya kamata al’umma su kasance masu kishinceton rayuka.

 

PUNCH

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending