Entertainment
An Yi Wa Fitacciyar Mawakiyar Iran Bulala 74 Saboda Waka Ba Tare Da Hijabi Ba
Wata kotu a ƙasar Iran ta yanke wa fitacciyar mawaƙiya, Parastoo Ahmadi, hukuncin bulala 74 bayan ta gudanar da wani kide-kide da aka watsa kai tsaye a shafinta na YouTube ba tare da sanya hijabi ba. Hukumomin ƙasar sun zargi mawaƙiyar da aikata abin da suka bayyana a matsayin karya dokokin tarbiyya da ɗabi’ar jama’a.
Baya ga hukuncin bulala, kotun ta kuma haramta mata fita daga Iran na tsawon shekaru biyu, tare da dakatar da ita daga gudanar da ayyukan fasaha da waka a cikin wannan wa’adin. Rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mutanen da suka taimaka wajen shirya wasan kwaikwayon sun fuskanci irin waɗannan hukuncin.
Ana Zargin Fashewar Bam A Kasuwa A Legas
An dai yada bidiyon wasan kwaikwayon a YouTube, inda ya jawo hankalin miliyoyin masu kallo tare da haddasa muhawara kan dokokin da suka shafi mata da harkokin fasaha a Iran.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da masu fafutukar kare ‘yancin faɗar albarkacin baki sun yi Allah-wadai da hukuncin, suna mai cewa ya saba wa ka’idojin kare haƙƙin bil’adama da ‘yancin bayyana ra’ayi. Masu sukar gwamnatin Iran sun ce lamarin na nuna ci gaba da tsaurara matakai kan mata da masu fasaha a ƙasar.
-
News4 days ago
Hukumar Kula Da Harkokin Shari’a Ta Tilasta Wa Alƙali Ritaya Kan Zargin Karɓar Cin Hancin Naira 250,000 A Kano
-
News5 days ago
Jigawa: Sama da Gine-gine 200 Sun Lalace Sakamakon Iska Da Ruwan Sama Mai Ƙarfi
-
News4 days ago
Wasu Fusatattun Matasa Sun Hallaka Wani Mutum Tare Da Kona Gawarsa Kan Zargin Satar Babur A Kano
