Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Ƙwayoyi Da Aka Ɓoye Cikin Kujerun Da Aka Shigo Da Su Daga Ƙasar Waje

Published

on

images (4)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wani lodin miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin kujerun zama na sofa da kuma hulunan mata na ado da aka shigo da su ƙasar nan.

Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na hukumar, Femi Babafemi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Lahadi.

“Ku Karɓi Kuɗinsu, Ku Kashe, Ku Zaɓi Wanda Kuka Ga Dama”  —Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa

Ya ce kamen na daga cikin nasarorin da jami’an hukumar suka samu a ci gaba da ƙoƙarin da suke yi na dakile safarar miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Bidiyon da Babafemi ya wallafa ya nuna yadda jami’an NDLEA suka buɗe manyan kwalayen da aka shirya kujerun sofa a ciki, inda suka gano wasu kunshe-kunshe na miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye a cikin kujerun.

A wani samame makamancin haka, jami’an sun gano miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin hulunan mata na ado, bayan sun yanke wasu sassan kayan da aka yi amfani da su wajen ɓoye su.

Advertisement

Haka kuma, bidiyon ya nuna wasu buhuna da aka rufe sosai, waɗanda ke ɗauke da busasshen ganyen da ake zargin miyagun ƙwayoyi ne, wanda jami’an suka ƙwato.

Hukumar ta ce wannan nasara na cikin ƙoƙarin da take yi na dakile hanyoyin da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da su wajen shigar da haramtattun kayayyaki cikin Najeriya da kuma fitar da su zuwa ƙasashen waje.

A shekarun baya, NDLEA ta sha samun miyagun ƙwayoyi da aka ɓoye cikin kayayyakin amfanin yau da kullum, ciki har da kayan ɗaki, huluna, takalma da kayan lantarki.

Masu safarar miyagun ƙwayoyin dai na amfani da irin waɗannan dabaru ne domin kauce wa binciken jami’an tsaro a tashoshin jiragen ruwa, filayen jiragen sama da sauran wuraren jigilar kayayyaki.

 

 

Advertisement

TVCNEWS

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending