Connect with us

News

Jami’an Yansanda Sun Kwato Shanu 39 Da Aka Sace Bayan Musayar Wuta Da Barayin Shanu A Kaduna

Published

on

IMG 20261108 WA0025 768x576 1794143774
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta daƙile harin wasu da ake zargin ɓarayi ne, tare da ƙwato shanu 39 da aka sace a ƙauyen Illa, da ke Ƙaramar Hukumar Igabi ta jihar.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na asubahin ranar Asabar, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai hari ƙauyen tare da sace shanun wasu makiyaya Fulani uku.

Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Ƙwayoyi Da Aka Ɓoye Cikin Kujerun Da Aka Shigo Da Su Daga Ƙasar Waje

A yayin harin, an harbi wani mutum mai shekaru 25, mai suna Abubakar a ƙafarsa.

Wannan na cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Mansir Hassan, ta fitar a ranar Lahadi.

Ya ce ’yan sanda sun samu kiran gaggawa daga Alhaji Yahaya Abubakar da misalin ƙarfe 5 na asuba, inda ya sanar da su faruwar lamarin.

Advertisement

Ya ce bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda, tare da ’yan sa-kai da mazauna yankin, suka haɗa kai wajen bin sahun waɗanda ake zargin zuwa cikin daji.

Jami’an sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargin, lamarin da ya tilasta musu barin shanun da suka sace tare da tserewa zuwa cikin daji.

Ana zargin wasu daga cikinsu sun samu raunukan harbin bindiga.

Rundunar ta ce an yi amfani da harsasai guda takwas yayin musayar wutar.

An garzaya da wanda aka harba zuwa Asibitin Koyarwa na Shika, inda yake samun kulawa.

Haka kuma, an mayar da shanun guda 39 da aka ƙwato ga masu su.

Advertisement

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Muhammad Rabiu, ya yaba wa jami’an tsaro da mazauna yankin bisa gaggawar da suka yi wajen daƙile harin.

Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta ci gaba da gudanar da ayyuka domin yaƙi da satar shanu da sauran laifuka a faɗin jihar.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending