News
Babbar Kotu A Abuja Ta Soke Takarar Atiku Abubakar Na Jam’iyyar ADC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta rushe shugabancin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, tare da soke dukkan matakan da shugabancin ya ɗauka, ciki har da zaɓen fitar da gwani da ya tsayar da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, 2026, inda ya bayyana kafa kwamitin riƙon ƙwarya na Sanata David Mark a matsayin matakin da ya saɓa wa doka.
Al’umma Ne Ke Da Ikon Zaɓen Shugabanni, Ba Jam’iyyun Siyasa Ba – Farfesa Fagge
Kwamitin dai shi ne ya jagoranci gudanar da zaɓen fitar da gwani da ya samar da Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC.
Hukuncin ya biyo bayan ƙarar da tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar na shiyyar Arewa maso Gabas, Nafiu-Bala Gombe, ya shigar, inda ya ƙalubalanci yadda Sanata David Mark da Rauf Aregbesola suka karɓi shugabancin jam’iyyar bayan murabus ɗin tsohon shugabanta, Cif Ralph Nwosu.
Mai ƙarar ya nemi kotun ta soke dukkan matakan da shugabancin Mark ya ɗauka, tare da hana shi da Aregbesola ci gaba da bayyana kansu a matsayin shugabannin jam’iyyar.
A cikin ƙarar mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025, kotun ta amince da buƙatun mai ƙarar, matakin da ka iya ƙara dagula al’amuran cikin gida na ADC gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sai dai sakataren jin daɗin jam’iyyar na ƙasa, Nkemakolam Ukandu, ya ce ADC za ta ɗaukaka ƙara domin ƙalubalantar hukuncin.
Hukuncin na zuwa ne a lokacin da jam’iyyar ke ƙoƙarin ƙarfafa matsayinta da shirye-shiryenta na tunkarar babban zaɓen 2027.
-
News4 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News1 day ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
-
News4 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
