Connect with us

News

 ’Yan Sanda Sun Gargaɗi ’Yan Siyasa Kan Lalata Kayan Kamfen Abokan Hamayyarsu Gabanin  Zaɓen 2027

Published

on

IGP Disu (1)
Advertisements
WhatsApp Image 2026 11 04 at 12.03.38 AM

Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan lalata fastoci, tutoci da allunan tallan kamfen na abokan hamayyarsu gabanin babban zaɓen 2027.

Rundunar ta ce duk wanda aka kama da hannu wajen lalata kayan kamfen na wani ɗan takara zai fuskanci hukuncin doka, ciki har da kama shi da gurfanar da shi a gaban kotu.

Jami’an Soja Ya Samu Kyautar N500,000 Bayan Ya Ƙi Karɓar Cin Hanci

A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta bayyana cewa ba za ta lamunci duk wani nau’i na rashin haƙurin siyasa ko lalata kayan kamfen da gangan ba.

Ta ce cire fastocin ɗan takara ko lalata su ba bisa ƙa’ida ba laifi ne na ɓarnatar da dukiya, wanda dokokin ƙasar suka tanadi hukunci a kansa.

Rundunar ta yi nuni da sashe na 451 na dokar manyan laifuka (Criminal Code Act) da kuma sashe na 326 na dokar Penal Code a matsayin dokokin da suka tanadi hukunci kan irin wannan laifi.

Advertisement

A wani mataki na tabbatar da bin doka, Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya umarci kwamishinonin ’yan sanda na jihohi 36 da na Babban Birnin Tarayya Abuja da su ƙara sanya ido tare da binciken duk wani rahoto da ya shafi lalata kayan kamfen.

Ya kuma umarce su da su tabbatar an gurfanar da waɗanda aka samu da laifin a gaban kotu.

Sanarwar ta ƙara da cewa gargaɗin ya shafi waɗanda ke ɗaukar nauyin aikata laifukan, da masu ɗaukar mutane aiki ko ba su kuɗi domin lalata kayan kamfen na abokan hamayyarsu.

Rundunar ta jaddada cewa dukkan jam’iyyun siyasa da ’yan takara suna da haƙƙin samun kariya daidai wa daida a ƙarƙashin doka.

Ta ce babu wani mutum ko ƙungiya da ke da ikon yanke hukuncin ko kayan kamfen na wani ɗan takara za a bari a nuna ko kuma a lalata.

Saboda haka, rundunar ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su mutunta haƙƙin abokan hamayya, su bi ƙa’idojin zaɓe tare da gudanar da kamfen cikin lumana domin tabbatar da zaman lafiya gabanin zaɓen 2027

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending