News
Gwamnan Kano Ya Nemi Sauya Kwamishinan Ƴansanda Da DPO 18 Gabanin Zaɓen 2027 —Rahoto

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nemi sauya kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Bakori, da kuma jami’an ’yan sanda 18 da ke jagorantar sassan rundunar a faɗin jihar, a cewar wani rahoto.
Jaridar Daily Nigerian ce ta wallafa rahoton, inda ta ce gwamnan ya zaɓi CP Mohammed Yusuf Adamu, wanda aka ƙara wa girma kwanan nan, domin maye gurbin CP Bakori.
Tinubu Ya Nemi Amincewar Majalisar Dattawa Kan Ciwo Sabon Bashin Dala Biliyan 7.7
Rahoton ya ce matakin ya biyo bayan rashin jituwa tsakanin gwamnan da kwamishinan ’yan sandan kan sauya wuraren aikin wasu jami’an rundunar.
Majiyoyin jaridar sun bayyana cewa CP Bakori ya sauya wasu DPOs, inda ya naɗa manyan jami’an da suka fi waɗanda aka cire girma da ƙwarewar aiki.
Sai dai gwamnan bai gamsu da wannan mataki ba, inda ya nemi a mayar da jami’an da aka sauya zuwa wuraren aikinsu na baya.
Bisa ga rahoton, an tura DPO 18 zuwa wasu jihohi, ciki har da Yobe, Gombe, Kebbi, Sakkwato, Zamfara da Katsina.
A nasa ɓangaren, kakakin gwamnan ya ce ba shi da masaniya kan batun.
Sai dai Rahoton bai bayyana ko rundunar ’yan sandan Najeriya ta tabbatar da wannan sauyi ba.
-
News3 days ago
Wasu ’Yanbindiga Sun Yi Garkuwa Kimanin Yara 12 A Neja
-
News3 days ago
Jami’an NDLEA Sun Kama ‘Yan Nijeriya Biyu Mazauna Turai Da Suka Haɗiye Ƙunshin Hodar Iblis Guda 200 A Filin Jirgin Abuja
-
News13 hours ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Shirin Farfaɗo Da Kamfanin Jirgin Saman Nigeria Air
