Connect with us

News

Dakarun Soji Sun Ceto Yarinya Mai Shekaru 16 Da Ta Tsere Daga Sansanin ’Yan Ta’adda A Borno

Published

on

IMG 20261104 104524 434
Advertisements
WhatsApp Image 2026 10 20 at 1.48.05 PM

Dakarun Sojojin Najeriya sun ceto wata yarinya mai shekaru 16, Hajara Haruna, bayan ta tsere daga wani sansanin da ake zargin mayakan ’yan ta’addan Wa’a ne ke amfani da shi a tsaunukan Mandara, da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza ta Jihar Borno.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa an ceto yarinyar ne a ranar 2 ga Nuwamba, 2026, lokacin da dakarun Bataliya ta 192, ƙarƙashin Birged ta 26 ta Rundunar Sojin Ƙasa, suka gano ta a kusa da ƙauyen Hudugum, a yankin Hambagda, kan hanyar Gwoza zuwa Limankara.

Jami’an EFCC Sun Gano Matatar Man Fetur Da Wasu ‘Yan China Ke Gudanarwa A Ogun

Binciken farko ya nuna cewa yarinyar ta tsere ne daga wani sansani da mayakan Wa’a ke amfani da shi a tsaunukan Mandara.

Bayan ceto ta, sojojin sun miƙa ta ga ofishin kula da sansanin ’yan gudun hijira na cikin gida (IDP) da ke Gwoza, domin samun taimako da kulawar da ta dace.

 

Advertisement

ZAGAZOLA MAKAMA

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending